Kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya gudanar da taron tattaunawa tare da wakilan da ba na JKS ba, domin neman ra’ayi da shawarwari kan yanayin tattalin arziki na bana da aikin tattalin arziki na shekarar 2025.
Babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jagoranci taron tattaunawar a ranar 6 ga watan Disamban nan, inda ya gabatar da muhimmin jawabi. Yana mai cewa, yayin da a shekarar 2025 kasar za ta kawo karshen shirin tsare-tsare na shekaru biyar karo na 14 wato (2021 zuwa 2025), ya zama wajibi a aiwatar da manufofin sassan tattalin arzikin masu inganci da tasiri.
- Sin: Daga 2018 An Gurfanar Da Mutane 114,000 Kan Laifuka Masu Nasaba Da Amfani Da Mukami Ba Bisa Ka’ida Ba
- Inuwar Gamji
Hakazalika, Xi ya yi kira da a fadada bukatun cikin gida, da sa kaimi ga dunkulewar ci gaban kirkire-kirkiren fasahohi da masana’antu, da daidaita kadarori da kasuwannin hannayen jari, da hanawa da warware hadarurruka a muhimman wurare da matsin lamba daga waje.
Shugabannin kwamitocin koli na jam’iyyu takwas da ba na JKS ba, da shugaban kungiyar gamayyar masana’antu da kasuwanci ta kasar Sin (ACFIC), da wakilin jama’a da ba sa cikin jam’iyya su ma sun gabatar da jawabai. Kana sun amince da nazarin da kwamitin kolin JKS ya yi kan halin da ake ciki na tattalin arziki da kuma tsare-tsare da batutuwan da suka shafi ayyukan tattalin arziki na shekarar 2025.
Sun kuma ba da shawarwari kan batutuwan da suka hada da gaggauta bunkasa sabbin karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko da karfafa ka’idojin sassan tattalin arziki yadda ya kamata. (Mohammed Yahaya)