Kwanaki hudu da kai harin ta’addanci a garin Mafa da ke karamar hukumar Tarmuwa, wasu da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne sun sake kai hari Goni Madu da ke karamar hukumar Buni Yadai Gujba a jihar Yobe inda suka bude wa sansanin ‘yan banga wuta bayan sun masa kawanya.
Da yake zantawa da LEADERSHIP ta wayar tarho, wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, maharan sun far wa Buni Yadai da misalin karfe 1 na dare na ranar Laraba.
- Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Ƙarin Naira Biliyan 99.2 Cikin Kasafin Kuɗin Jihar
- Farashin Kayayyaki Zai Sake Tashi A Nijeriya – MAN
A cewar mazaunin garin, ‘yan ta’addan da yawansu ne suka mamaye garin inda suka wuce kai tsaye zuwa sansanin ‘yan banga tare da bude masa wuta.
Wani dan banga da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce, maharan sun kona daukacin harabar ‘yan bangan tare da lalata duk kayayyakinsu.
Wani dan banga mai suna Goni Modu wanda ya samu rauni daga harsashin maharan, wanda a halin yanzu haka ke kwance a babban asibitin Damaturu yana jinya, ya ce ba a samu asarar rai ko daya ba yayin harin.