Bayanai sun nuna cewa tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na tattaunawa da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan yiwuwar komawarsa cikin jam’iyyar mai mulki.
Majiyoyi daga shalƙwatar APC a Abuja sun tabbatar da cewa tattaunawa tsakanin Kwankwaso da shugabancin jam’iyyar ta yi nisa, bayan ganawarsa da fadar shugaban ƙasa. Wasu na cikin jam’iyyar sun ce Kwankwaso ya miƙa wasiƙa zuwa shalƙwatar APC a Abuja, inda ya zayyana sharuɗɗan dawowarsa, ciki har da tabbatar da cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya samu tikitin APC a zaɓen 2027.
- Kwankwaso Ya Gana Da Shugabannin NNPP A Kuros Ribas Don Tunkarar Zaɓen 2027
- Tinubu Ya Ci Amanar Kano, Babu Batun Haɗin Guiwa Tsakaninsa Da Kwankwaso A 2027 – Galadima
Sai dai wasu jagororin APC a Kano sun bayyana cewa wasiƙar ba ta iso hannunsu ba, saboda rikicin siyasa da ya daɗe tsakanin Kwankwaso da shugabannin jam’iyyar a jihar. Duk da haka, sun ce idan ya dawo jam’iyyar, babu wanda zai hana shi shiga, tunda ya kasance ɗan siyasa mai tasiri a Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
A makon da ya gabata, Kwankwaso ya bayyana cewa ba ya ƙin haɗa kai da APC, amma ya jaddada cewa dole a fayyace amfanin da NNPP za ta samu idan aka yi haɗin gwuiwa. A cewarsa, jam’iyyarsa na da cikakkun tsare-tsare da ‘yan takara a duk jihohi, don haka ba za ta shiga ba tare da ƙwaƙƙwarar yarjejeniya ba.
A gefe guda, manyan shugabannin APC daga Kano sun gudanar da taro a Abuja, inda suka haɗa kai wajen goyon bayan wa’adi biyu na Shugaba Bola Tinubu, tare da ƙudurin tabbatar da cewa jam’iyyar ta ƙwato mulkin Kano a zaɓen 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp