Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi Gwamnan Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, a daren Lahadi a gidansa da ke Abuja, inda gwamnan ya kai ziyarar ban-girma tare da miƙa masa kyautar girmamawar da aka ba shi kwanan nan. A cewar sanarwar mai magana da yawun Kwankwaso, Saifullahi Hassan, gwamnan ya je tare da tawagar gwamnatin jihar Kano.
A ganawar, Gwamna Yusuf ya gabatar da lambar yabo ta Distinguished Award for Visionary Leadership and Public Service Sector Reform da aka ba shi a bikin Nigeria Excellence Awards in Public Service (NEAPS) da aka gudanar a Abuja. Sanata Kwankwaso ya taya shi murna bisa wannan babbar nasara da ta nuna jagoranci na zahiri da sauye-sauyen da ake gani a Kano.
- Da Ɗumi-ɗumi: Ƙungiyar Likitoci Ta Janye Yajin Aiki Bayan Shafe Kwanaki 29
- Sharuɗɗan Da Sule Lamido Ya Gindaya Wa Jam’iyyar PDP A Wa’adin Kwana 10
Kwankwaso ya bayyana alfahari da irin jagorancin da gwamnan ke bayarwa, yana jaddada cewa lambar yabon ta nuna tasirin ci gaba da ake samu ga al’ummar Kano da ma Najeriya gaba ɗaya. Ya kuma yi masa addu’a tare da fatan ya ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi jin daɗin jama’a.














