Masanan kasar Amurka da dama suna ci gaba da yin kira ga gwamnatin Biden, da ta soke harajin da aka sanya a lokacin gwamnatin Trump kan kayayyakinn da ake shigo da su daga kasar Sin, inda suka jaddada cewa, kawo karshen yakin ciniki a tsakanin kasashen Sin da Amurka zai yi matukar amfanawa Amurka.
Anton Bekkerman, wani masanin tattalin arzki a fannin aikin gona, kana darakta cibiyar nazarin aikin noma ta jahar New Hampshire ya ce, “lokaci ya yi da ya kamata a fara tunanin yadda za a ci gaba, maimakon kirkiro wani abin da zai mayar da hannun agogo baya,” a cewar masanin, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban sashen nazarin kimiyyar rayuwa da aikin gona a jami’ar New Hampshire.
Ya ce, kara kudaden harajin kwastan ba manufofi ne masu alfanu ba, kamar yadda ya bayyana a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya-bayan nan.
Shi ma a nasa bangaren, Vincent Smith, masanin tattalin arziki a fannin aikin gona, kana shehun malamin jami’ar Montana, ya bayyana a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, “Za a iya bayyana takaddamar kasuwancin a matsayin wani babban koma bayan tattalin arziki da gwamnatin Trump ta aiwatar, saboda abin takaici ne da rashin tunani game da hakikanin yadda duniya ke gudana, wanda wasu daga cikin mashawartan tsohon shugaban suka dinga ingiza jagoran kasar na wancan lokaci.”
Tun da farkon wannan shekara, wasu alkaluman da sashen ayyukan gona na Amurka ya fitar sun nuna cewa, yakin cinikin da gwamnatin Trump ta assasa, ya jawowa aikin gonar Amurka hasarar dalar Amurka kusan biliyan 27 a cikin shekaru biyun da suka gabata.(Ahmad)