Yawan amfani da magungunan kula da lafiyar dabbobi barkatai, ciki har da bangaren kiwon kifi, na ci gaba da jefa fargaba a fannin kiwon lafiyar al’ummar daukacin Nijeriya.
Masu kiwon, na bai wa dabbobinsu magunguna ne, ba tare da neman shawarar likitocin dabbobi ba, inda lamarin ke haifar da illa ga naman dabbobi da kuma kwan kajin gidan gonar da ake kiwatawa, domin kasuwanci tare kuma da illa ga madarar shanu.
- Gwamnati Ta Amince Da Bai Wa Jami’o’i 11 Masu Zaman Kansu Lasisi
- Masana Kimiyya Na Sin Sun Gano Tsare-Tsaren Rayuwa A Muhallin Halittu Mafi Zurfi A Teku
Magungunan warkar da dabbobin dai, na taimakawa wajen yakar kwayoyin cututtukan da ke harbin dabbobi, wanda yawan bai wa dabbobin magungunan ke jawowa su daina yin aiki a jikin dabbobin da suka kamu da kwayoyin cutar.
Kazalika, kwararru a fannin kiwon lafiyar dabbobin sun ce, yawan bai wa dabbobin magungunan, na shafar lafiyar Bil’adaman da ke cin naman dabbobin.
Daya daga cikin kwararrun, kuma Darakta a Cibyar Binken Lafiyar Dabbobi ta Kasa (NBRI) da ke Jihar Filato, Dakta DSati Ngulukun, ya shaida wa Jaridar LEADERSHIP Hausa yadda wasu masu kiwo kan dogaro a kan rade-radi da rashin yin amfani da shawarar kwararru a bangaren kula da lafiyar dabbo, musamman wajen bai wa dabbobinsu magunguna, bayan sun harbu da wasu kwayoyin cututtuka.
“Wasu masu kiwon, suna zuwa shagunan sayar da magani ne su sayo su rika bai wa dabbobin da suka harbu da wata kwayar cuta, ba tare da yin la’akari kan adadin magungunan da ya kamata su ba su ba”, in ji Ngulukun.
Ana kuma bukatar masu kiwon su dakar da bai wa dabbonin nasu magunguna daidai da lokacin da misali, kajin gidan gona ke shirin fara yin kwai ko kuma lokacin da shanu ke shirin fara samar da madara, domin kare lafiyar mutane.
Sai dai, abin takaici shi ne, akasarin masu kiwon; ba sa kiyaye irin wadannan lokuta, wanda hakan ke shafar lafiyar mutanen da suka yi amfani da irin wadannan dabbobi.
Kazalika, yawan bai wa dabbobin magungunan barkatai don yakar wasu kwayoyin cutar da ta harbe su, na iya sanya wa ko da an bai wa dabbobin magungunan, su ki yin wani amfani a jikinsu.
Har ila yau, duk da cewa; an samar da dokoki a kan wannan matsala, sai dai, ana ci gaba da samun sakaci wajen tilasta kiyayewar yawan shayar da dabbobin magungunan barkatai, ba tare da masu kiwon sun samo shawarar Likitocin dabbobin ba.
A cewar wasu kwararru a fannin, wannan matsalar na jawo karuwar mutuwar dabbobi tare kuma da jawo asara ga masu kiwonsu.
A yanzu haka, saboda wannan batu na bai wa dabbobin magunguna, hakan ya jawo bijirewar da kwayar cutar ke yi na haifar da mutuwar dabbobi a duk shekara da yawansu ya kai kimanin miliyan 4.95, inda mafi akasari aka fi alakanta mutuwar tasu kai tsaye da kimanin miliyan 1.27, inda kwararrun suka yi gargadi da cewa, idan har ba a dauki matakan da suka dace ba, nan da 2050, adadin mutuwar dabbobin zai kara rubanya zuwa miliyan 10.
Bugu da kari, Nijeriya na daga cikin kasashen da ake fuskantar irin wannan matsala, inda aka alakanta mutuwar akalla duk shekara kimanin 263,400, sakamakon rashjin jin magani da kwayoyin cutar da ke harbin dabbobin ke yi.
Wani kwararre a bangaren kula da lafiyar dabbobi, Dakta Nafiu Lawal, ya shaida wa jaridar LEADERSHIP cewa, ba a mayar da hakankali wajen wayar da kan masu kiwon dabbobin kan wannan matsala.
Dakta Nafiu, ya shawarci masu kiwon dabbobin da su rika tuntubar kwararrun likitocin dabbobi, domin samun shawarwari kan irin magungunan da ya kamata su rika bai wa dabbobin nasu, bayan sun kamu da kwayoyin cututtuka.
Sama da shekaru takwas da suka gabata, Nijeriya ta samar da tsare-tsare na kasa guda biyu a bangaren kiwo, ciki har da yadda za a dakile wannan matsala.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp