Hukumar Kwastam reshen Jihar Katsina ta samu nasarar kama buhuna goro da wasu kaya da aka haramta shigo da su cikin kasa da aka kiyasta kudaden u ya kai Naira Miliyan 38.5 a tsakanin watan Afrilu zuwa yanzu.
Shugaban hukumar na yankin Katsina, Comp. Dalha Wada-Chedi ya sanar da haka a jawabin da ya yi wa manema labarai ranar Alhamis a birnin Katsina.
- Mata Sun Yi Zanga-zanga Kan Yawan Bacewar Kananan Yara A Taraba
- Tinubu Ya Mika Wa INEC Sunan Mataimakinsa Sai Dai Bai Bayyana Sunan A Fili Ba
Dalha-Chedi ya kara da cewa, kayan da aka cafke bai kai na lokutan baya ba, wannan kuma ya faru ne sakamakon yadda gwamnatin tarayya ta bude iyakar Nijeriya ta garin Jibiya wanda hakan ya haifar shigo da kaya ta ka’ida da ‘yan kasuwa suke yi.
Wada-Chedi ya ce kayayyakin sun hada da buhunan shikafa 715 da aka kiyasta kudin su ya kai Naira Miliya 18.7 da motoci 7 da babur 8 wanda aka kiyasta kudinsu ya kai Naira miliyan 8.
“Sauran kayayyakin sun hada da taliya ta Naira Miliyan 2.4 da madara ta Naira Miliyan 1.2 sai kuma goro na Naira Miliyan 1.1.