Hukumar Kwastam ta Nijeriya da ke kula da daukar kaya a filin jirgin Murtala Mohammed ta kama Mazakutar Jaki 7000 da ake kokarin fitarwa zuwa Hong Kong.
Shugaban Hukumar Kwastam na yankin, Sambo Dangaladima ya bayyana hakan a lokacin da yake baje kolin buhunan mazakutar Jakunan guda 16 ga manema labarai da kudin harajin kayan ya kai Naira Miliyan 216, 212, 813.
“Masu fitar da kayan, sun bayyana wadannan haramtattun sassan namun dabbobin a matsayin cewa, mazakutar Sanuwa ce , bayan tantancewa, jami’an mu sun gano cewa mazakutar Jaki ce, wannan shi ne karon farko da muka kama irin wannan abu. ba za mu bari irin wannan haramtacciyar fataucin namun daji ya bunkasa a karkashin mu ba,” Inji Dangaladima.
An mika kayan da aka kwace ga hukumar kula da ayyukan noma ta Nijeriya wanda mataimakin Sufritanda, Adebimpe Adetunji ya wakilta.
Bayan haka, rundunar ta mika kwalaye 912 na magunguna jabu (ba tare da lambar rijistar NAFDAC ba) da aka shigo da su daga Pakistan ga hukumar kula da abinci ta kasa wanda Jami’in Ayyuka na Hukumar SAHCOL, Hassan Yusuf ya wakilta.
Hukumar Kwastam ta kuma mika kwalaye 1158 na Tramadol ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA.