Jami’an Hukumar Hana Fasa-Kwauri ta Kasa (NCS), a Jihar Katsina sun kama wasu mutane hudu da ake zargi yin safarar kayayyaki a jihar.
Duk da cewa an bayar da belin wadanda ake zargin har sai an kammala bincike, hukumar kwastam ta Jihar Katsina ta danganta nasarorin da aka samu a cikin wannan lokaci da ake bitar da su da jajircewa da jami’an rundunar suka yi tare da hadin gwiwar saura hukumomin tsaro.
- ‘Yan Daba Sun Afkawa Gidan Wani Mai Goyan Bayan Atiku Sun Masa Ta’addanci A Jihar Ribas
- Hukumar Kwastam Ta Kwace Litar Man Fetur 85,300 A Jihar Ogun
Kwanturolan hukumar kwastam mai kula da Jihar Katsina, Dalha Wada Chedi ne, ya bayyana hakan a ranar Talata a hedikwatar rundunar da ke Katsina yayin taron manema labarai na wata-wata da rundunar ta gudanar kan ayyukan da ta ke yi.
Chedi a yayin da yake baje kolin wasu kayayyakin da rundunar ta kama, ya yi kira ga al’ummar jihar da ‘yan kasuwa da su yi amfani da damar da aka sake bude kan iyakar Jibiya domin gudanar da harkokinsu na kan iyaka.
Ya kara da cewa har yanzu sauran kan iyakokin na rufe, don haka wucewa ko yunkurin wuce gona da iri ya sabawa doka saboda ingantacciyar manufar Gwamnatin Tarayya ta rufe iyakokin.
“Yayin da muke dosar shekara mai kamawa, rundunar za ta ci gaba da samar da dabarun tattara bayanan sirri masu karfi a kan tsaron kan iyaka da tabbatar da ingantaccen yanayi na hada-hadar kasuwanci tare da inganta hanyoyinmu na yaki da fasa-kwauri domin murkushe abubuwan da aka yi fasakwaurin wanda ke haifar da babbar barazana ga tattalin arziki da tsaron kasar nan,” in ji shi.
A cewar Kwanturolan na Kwastam, rundunar ta samu N179,206,288.33 a hannun wadanda suka shiga hannu.
Ya nuna karin Naira miliyan 58 daga miliyan 121,800,478.00 da aka tara a watan Oktoban 2022, wanda ke nuna karin kashi 47% na kudaden shiga da aka tara.
A lokacin da ake bitar rundunar, ya bayyana cewa, motocin da aka kama masu fasa-kwaurinsu da hanyoyin jigilar kayayyaki kamar buhunan shinkafa 239 na kasar waje mai nauyin kilogiram 50 kowanne da kudin harajin N7,098,300.00, buhu biyu na shinkafar kasar waje mai nauyin kilogiram 25, sai katan-katan guda 821 na taliyar kasar waje.
Ya ce hukumar za ta ci gaba da yaki da fasa-kwaurin kayayyaki daga kasashen ketare.