A ranar Alhamis ne hukumar Kwastam (NCS) da ke aiki a filin jirgin saman Murtala Muhammed (MMIA) da ke Ikeja a Legas ta mika takardun kudi na bogi na Dala miliyan 1.2 da na’urorin kirifto guda biyar ga Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC).
Rundunar ta kuma mika wasu jirage marasa matuka guda 148; makamai da sauran kayayyakin aikin soji 112; hular tare harsashi guda biyu da singileti ta Sojoji guda biyu ga runduna ta 81 na sojojin Nijeriya da ke Legas.
- Kwastam Reshen Tashar Jiragen Ruwan Apapa Ta Tara Naira Biliyan 489 Cikin Wata Uku
- Tsaron Yanar Gizo: TUC Ta Yi Barazanar Shiga Zanga-zanga A Nijeriya
An mika jabun kudin ne ga mataimakin kwamandan hukumar EFCC, Oguzi Moses, yayin da sauran kayayyakin na aikin soji aka mika su ga babban kwamandan runduna ta 81 ta Nijeriya, Manjo Janar Muhammad Usman.
Da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan hukumar NCS daga watan Janairu zuwa Afrilu 2024, Kwamandan Kwastam na yankin (CAC), Kwanturola Charles Orbih, ya ce, an mika kayayyakin da aka kama ne bisa umarnin Kwanturola Janar na Hukumar, Bashir Adewale Adeniyi.