Mukaddashin Kwantirola Janar na hukumar Kwastam na kasa (NCS), Bashir Adewale Adeniyi, ya zayyana ka’idojin da da za a bi kafin sake bude iyakokin Nijeriya.
Bashir ya bayyana hakan ne yayin da yake yi wa jami’in hukumar jawabin a lokacin da kai ziyarar aiki a rundunar hukumar ta 1 da ke a yankin Idiroko a jihar Ogun.
A cewarsa, hukumar za ta yi nazari a kan wasu tsare-tsarenta, idan yankunan sun ci gaba da bin doka da oda akan abin da ya shafi shigo da kaya zuwa cikin kasar nan da kuma fitar tare da fitar da su.
Ya ci gaba da cewa, daya daga cikin tsare-tsaren shi ne na sake yin nazari a kan tsarin tura man fetur zuwa ga gidajen sayar da mai wadanda suka kasance kilomita 20 da iyakokin Nijeriya.
Ya ce, akwai abubuwa da dama da alumomin suka bukata, inda wasu daga cikinsu, sun fi karfin nauyin da gwambatin tarayya ta dora wa hukumar, domin wasu tsare-tsaren nauyin mahukuntan kasar nan ne.
Sai dai, ya bayar da tabbacin cewa, nuna kan yin aiki da sauran mahukuntan kasar nan za mu kuma gabatar da bukata don yin nazari akan wadanan tsare-tsaren.
Kazalika, ya bayyana cewa hukumar za ta bayar da shawara domin a yi nazari a kan shigo da ababen hawa zuwa cikin kasar, ganin cewa an cire tallafin man fetur, inda ya ce mun kuma gabatar da bukatar sake yin nazari a kan dakatar da gidan man fetur da ke a iyakon Nijeriya.
Bugu da kari, mukaddashin ya kuma umarci jami’in rundunar ta Ogun da su kara jajircewa wajen tabbatar da tsaro a iyakokin kasar.
Ya sanar da cewa, musamman ganin cewa, iyakar ta Idiroko, ta kasance iyaka mafi sauki da ake shigo wa kasar har da shigo wa Jamhuriyar Benin.
A cewarsa, “ba za mu zura ido mu bari ana aikata manyan laifuka a iyakokin kasar mu ba.”