ALHAJI IBRAHIM MU’AZZAMU MABO, Shugaban Kungiyar ‘GAWUNA HAS COME’ na Jihar Kano, gogaggen dan kasuwa, mai fashin baki a kan harkokin ci gaban Jihar Kano da harkokin kasuwanci, sannan makusanci ga Dakta Nasiru Yusif Gawuna, wanda kotun sararon kararrakin zabe da ta daukaka kara suka ayyana a matsayin halastaccen Gwamnan Jihar Kano, ya wakilinmu na Kano; ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, kan dalilan kafa kungiyar ‘Gawuna Has Come’, da sauran abubuwan da kungiyar ke hasashe kan makomar Kano a nan gaba kadan. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:
Da farko, da wa muke tare?
Alhamdulillahi! Muna kara godiya ga Allah. Sunana Alhaji Ibrahim Mu’azzamu Mabo Sani Mainagge, an haife ni a Unguwar Sani Mainagge, na yi karatun firamare a Sani Mainaggen; daga nan na wuce zuwa GATC Gwale, sai kuma Makarantar Hadaka ta Gwamantin Tarayya da ke Karaye.
Daga nan kuma na sake wucewa Makarantar Share Fagen Shiga Jami’a ta Kano (CAS), kazalika, na halarci Makarantar Nazarin Harkokin Shari’a ta Aminu Kano ‘School for Legal studies’, inda na karantar harkokin shari’a, daga nan ne kuma sai na tsallaka zuwa Jami’ar Al-Lahada da ke Kasar Nijar, inda na yi sa’ar samun digirina na farko a kan harkokin shari’a. Bayan nan ne kuma, sai na tsunduma harkokin kasuwanci, wanda kuma yanzu haka ni ne Shugaban Kungiyar ‘Gawuna Has Come’ na Jihar Kano.
Duba da yanayin tarihinka, yaya aka yi ka tsinci kanka a harkokin siyasa?
Masha Allah, kamar yadda ka sani ne akwai dalilai da dama wadanda ke sa mutum tsunduma cikin harkokin siyasa. Amma magana ta gaskiya, ni tun tasowata ina da ra’ayin tallafa wa jama’a, domin kuwa tun shekara 13 da suka gabata na kirkiri wata gidauniya, wadda na sanya wa suna Gidauniya IMY (IMY FOUNDATION), wadda na fara tallafa wa marayu da masu karamin karfi a karkashinta, ta hanyar kula da harkokin rayuwa da kuma karatunsu.
Ko ka taba samun kanka a wasu kungiyoyi na dalibai, wadanda suka haska maka shiga wannan gwagwarmaya ta siyasa?
Ko shakka babu, an samu kai a cikin ire-iren wadannan kungiyoyi, domin kuwa an dan taba su gwargwadon iko, wannan tasa ganin yadda muka mu’amalanci marayu da masu karamin karfi, ya ba mu damar kallon yadda za mu samu damar fadada irin wannan mu’amala, wadda hakan tasa muka ga dacewar tsunduma wadannan harkoki na siyasa.
Ko masu karatu za su iya jin dalilin kafa kungiyar ‘Gawuna Has Come’?
Kasancewar Siyasar Kano na da alaka da tarbiya da addininmu, wannan tasa muka kafa wannan kungiya, wadda muka mayar da hankali a kan batun addu’o’i, wadda ko shakka babu ita ce takobin duk wani mai fatan samun ingantacciyar nasara. Sannan, mun fara da gudanar da addu’o’i a kan siyasara Dakta Nasiru Yusif Gawuna, kamar yadda aka sani tarbiyyarsa ta nuna yadda ya fi bukatar addu’a, bayan yin dogon nazari a kan haka; sai muka ga dacewar tattaro mutanen da muka aminta da shahadarsu a kan tafiyar Gawunan, wadanda muke da tabbacin za su ba mu gudunmawar addu’o’i, don haka gaskiyar magana da haka muka fara.
Har ila yau, ganin yadda kotu ta ayyana Dakta Nasiru Yusif Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Kano, sannan tunda wadancan ba su hakura da hukucin kotun farko ba, ya sa muka mai da hankali tare da rada wa wannan kungiya suna na ‘Gawuna Has Come’, domin ci gaba da yin luguden addu’o’i, domin dorewar wannan nasara.
Shin kai ne ka rada mata wannan suna ta kai ga nada ka a matsayin shugabanta?
Magana ta gaskiya ba ni ne na rada mata wannan suna ba, kasnacewar a kwai mutane masu kima da hangen nesa ya sa aka samar da wannan suna, sannan kuma ba ni ne na nada kaina a matsayin shugaban wannan kungiya ba, ganin cancantata ya sa aka aminta da na rike shugabancinta a matsayin rikon kwarya.
Haka zalika, idan ka dubi harkokina ka san zai yi wuya a ce na kuma hada da wannan shugabanci, amma saboda karfin tafiyar ya sa na ajiye dukkanin wasu abubuwa nawa a gefe guda na mayar da hankali a kan wannan lamari na harkokin addu’a gwargwadon iko, sannan kuma Alhamdulillahi; muna ganin nasara kwarai da gaske.
Mene ne ya bai wa Mabo sha’awar hada tafiya Dakta Gawuna?
Sanina da Gawuna ba na yanzu ba ne, domin kuwa na san shi tun lokacin da ya fara zama a unguwarmu ta Dandago, sannan kamar yadda ka sani ne tsakanin Dandago da Sani Mainagge tazarar babu yawa, har ila yau na san yadda ya zauna da iyayenmu lafiya ga kuma kyakkyawar tarbiyya da girmama na gaba, wannan tasa nake da yakinin cewa matukar Allah ya rabauta Kano da shi, ko shakka babu za ta hau saiti dodar ba tare da wata lankwasa ba.
Me ya sa kake ganin shi ya fi dacewa da samun wannan dama?
Ai wannan duk wani mai kyakkyawan tunani ya san Gauwna shi ne mafi dacewa da mulkin Kano a daidai irin wannan lokaci, musamman ganin yadda wadancan mutanen suka haifa wa jihar matsaloli, musamman a bangaren yadda suka hargitsa nutsuwar wasu daga cikin ‘yan kasuwa ta hanyar rushe musu guraren neman halaliyarsu.
Wannan ne ya sa muke da yakinin cewa, idan Allah ya mika wulayar Jihar Kano da Kanawa a gare shi, ko shakka babu za a yi matukar farin cikin gaske, wannan tasa muka tashi tsaye domin ci gaba da yin luguden addu’o’i, sakamakon muna da yakinin yana daga cikin sunnar Alllah addu’ar wanda aka zalunta karbabbiya ce. Don haka, wannan kyakkyawar manufa ta wannan kungiya ce ta sa dumbin mutane masu daraja da kima ke yin tururuwa wajen shigowa cikinta, wanda hakan ya ke baiwa kowa mamaki.
Ko batun rusau da aka yi wa ‘yan kasuwa na cikin dalilan da suka sa Mabo zabar shiga wannan shiri na gudanar da addu’o’i?
Kwarai kuwa, ai wannan ko kadan ba abun mamaki ba ne idan hakan ya sa ni shiga, domin kowa ya san yadda Kano ta shahara ta fuskan kasuwanci, sai kuma ga gwamnati ta zo da wani tsari na kassara harkokin kasuwancin da ‘yan kasuwa. Don haka, kenan ka ga ya zama wajibi mu fito mu yi addu’a tare da fatan Allah ya fatattaki wadannan mutane ya kuma kawo mana wadanda za su taimaki ‘yan kasuwa da harkokinsu na kasuwancin baki-daya.
Wace irin gudunmawa Alarammomi ke bai wa wannan kungiya, musamman ta fuskar addu’o’in da kuka sanya gaba?
Alhamdulillahi, muna kara yi wa Allah godiya, muna kuma kara gode wa wadannan Alarammomi da Mahaddata Alkur’ani, domin kuwa zuwa yanzu, mun samar da wasu rundunonin Alarammomi guda biyar-biyar a kowace karammar hukuma cikin Kananan Hukumomin Jihar Kano 44, wadanda a kullum muke tare da su, muke kuma ci gaba gaba yin addu’o’i na musamman a irin wannan lokaci da muke dakon hukuncin karshe daga kotun koli ta tarayya, wanda muka kwashe kwanaki 40 muna luguden addu’o’i da saukar alkur’ani mai girma, domin fatan Allah ya tabbatar da mana da nasarar Dakta Nasiryu Yusif Gawuna da Mataimakinsa Alhaji Murtala Sule Garo.
Shin ko akwai wani kalubale da ka fuskanta tun bayan kafa wannan tsari na yin addu’o’i?
Babu sahakka akwai wannan kalubale, domin wasu ma gani suke yi kamar mun yi kutse ne don biyan bukatar kanmu, wanda kuma gaskiya ba haka lamarin yake ba, mu Kanon ce a gabanmu muka ita muke kallo da makomarta, sakamakon yakinin da muke da shi na cewa, idan Allah ya kawo Gawuna; ko shakka babu Kano za ta dauki irin saitin da ya kamata.
Haka zalika, kalubalen daga ko’ina akwai shi; cikin gida da waje kuma babu abin da ke gabana da ya wuce isowar Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, sannan ba na kallon duk wata hamayarsu; domin kuwa ba ta gabana, abin da ma nake kallo shi ne kamar so ake yi a kawar da hankalinmu daga harkar addu’o’in baki-daya, sakamakon irin nasarorin da ake samu.
Mene fatanka na karshe da za ka isra wa masu karatu?
Babban fatan da muke yi shi ne, Allah ya tabbatar wa da Dakata Nasiru Yusuf Gawuna da Mataimakinsa Murtala Suke Garo wannan nasara, sannan ina kara kira ga jama’armu; musamman Alarammomi da Mahaddata Alkur’ani cewa, su kara himma wajen ci gaba da yin wadannan addu’o’i, domin yanzu Gawuna ya fi bukatar addu’a, sannan bayan Allah ya tabbatar da shi a matsayin Gwamnanmu, mu sake kara addu’ar Allah ya kuma yi riko da hannunsa.