• English
  • Business News
Monday, May 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kyan Alkawari Cikawa

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Kyan Alkawari Cikawa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Daga ranar 13 zuwa 15 ga wata, an gudanar da taron kolin kasar Amurka da kasashen Afirka karo na biyu a birnin Washington, babban birnin kasar ta Amurka, wato shekaru 8 ke nan tun bayan da aka gudanar da taron a karo na farko. A shekarar 2014, gwamnatin Obama ta gudanar da taron karo na farko, inda kuma ya yi alkawarin karfafa huldar da ke tsakanin kasar Amurka da kasashen Afirka da ma gudanar da taron a kai a kai. Sai dai ba a yi zaton za a jima tsawon shekaru 8 kafin a kaddamar da taron a karo na biyu ba.

Kwana daya kafin a bude taron na wannan karo, Amurka ta lashi takobin samar da dala biliyan 55 cikin shekaru uku masu zuwa, don tallafa wa kasashen Afirka ta fannonin tattalin arziki da kiwon lafiya da tsaro da sauransu. Daga bisani, ta kuma sanar da habaka kawancenta na binciken sararin samaniya don shigar da wasu kasashen Afirka a ciki, baya ga kuma bayyana goyon bayanta ga shigar da kungiyar tarayyar Afirka cikin kungiyar G20.

  • Bangaren Sin: Ya Kamata Kasashe Masu Sukuni Su Cika Alkawarin Zuba Jari A Fannin Sauyin Yanayi Ga Kasashen Afirka

Babu shakka, abubuwan alheri ne ga kasashen Afirka. Amma ana nuna shakku a kan alkawuran, sakamakon yadda gwamnatin Amurka ta kasa cika alkawuran da ta dauka a gun taron da aka gudanar karo na farko a shekarar 2014. A lokacin, gwamnatin Amurka ta dauki alkawura da dama, amma ga shi bayan taron, a maimakon ta cika su sai ta rage kudaden jarin da ta zuba wajen yaki da cutar kanjamau a Afirka, tare da rage gudummawar da ta samar a shiyyar. Idan ba a manta ba kuma, gwamnatin Amurkar ta sanar da jerin shirye-shirye na tallafi, ciki har da “samar da lantarki a Afirka”, wanda ya yi alkawarin samar da wutar lantarki da suka kai MW dubu 20 ga kasashen Afirka ya zuwa shekarar 2020, amma kawo karshen shekarar 2020, lantarkin da aka samar bai kai kaso 1/4 na abin da ta alkawarta ba. Sabo da haka, idan gwamnatin Biden na son sake samun imani daga kasashen Afirka, dole sai ta cika alkawuran da aka dauka a baya tukuna.

Mene ne dalilin da ya sa Amurka ke son daukar alkawura amma ba tare da cikawa ba a gaban kasashen Afirka? In mun yi nazari, za mu ga cewa ainihin abin da ya sa take bunkasa alakarta da kasashen Afirka shi ne don su taimaka wajen ja-in-ja da take da wasu manyan kasashe, a maimakon a ce ta mai da su abokan hadin gwiwa na zaman daidaito da kuma cin moriyar juna, ballantana ta mai da hankali a kan daidaita matsalolin da ke ci musu tuwo a kwarya.

Wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma sun ce, a gun taron na wannan karo, jami’an kasar Amurka sun mayar da hankali sosai wajen ganin bakin na Afirka, ba su ji kamar ana matsa musu su yi zabi tsakanin “mu ko su” ba. Amma furucin da ministan tsaron kasar Lloyd Austin ya yi a wajen taron, ya tona mana ainihin abin da take neman cimmawa, inda ya ce, a yayin da Sin da Rasha ke kara taka rawa a harkokin nahiyar Afirka, kasashen biyu ka iya “lalata kwanciyar hankalin nahiyar”.

Labarai Masu Nasaba

Fasahar Shayi Ta Sin Ta Samar Da Kwanciyar Hankali Da Nishadi Ga ‘Yan Nijeriya

Xi Jinping Ya Taya Murnar Bude Bikin Baje Kolin Kayayyaki Na Yammacin Sin

To, kasashen Afirka sun san wane ne aminansu na gaskiya, haka kuma suna sane da abin da Amurka ke neman cimmawa. Don kafin taron, shahararriyar cibiyar nazarin manufofin diplomasiyya ta kasar Afirka ta kudu da aka san ta da sunan “The Institute for Global Dialogue of South Africa” ta fitar da rahoton cewa, ita kanta Amurka ce ke amfana da manufofin da ta samar kan Afirka, kuma ta gaza cika alkawuran da ta dauka, wadda take neman karfafa babakere a nahiyar Afirka da sunan dimokuradiyya. Rahoton ya kuma bayyana cewa, kwatankwacin yadda Amurka ke son kafa babakere da ma ba da lacca, kasar Sin ta fi samun karbuwa a kasashen Afirka sakamakon irin matsayinta na rashin tsoma baki cikin harkokin gida da ma samun moriyar juna a yayin da take hulda da kasashen Afirka.

A yayin da ake fuskantar munanan tasirin annobar Covid-19 da rikicin Rasha da Ukraine da ma sauyin yanayin duniya ke haifarwa ga tattalin arziki da zaman al’umma, kasashen Afirka na matukar son ganin a samar musu tallafi da gudummawa wajen fuskantar matsalar karancin abinci da ta tattalin arziki, kuma a hakika, Amurka na iya samar da taimakonta. Kasar Sin a nata bangaren na son ganin karin kasashen da suka hada da Amurka sun ba da gudummawarsu ga Afirka, haka kuma tana fatan Amurka za ta dauki hadin gwiwarta da kasashen Afirka yadda ya kamata. Daidai kamar yadda jakadan kasar Sin a Amurka mista Qin Gang ya bayyana a kwanan baya cewa, “Ya kamata nahiyar Afirka ta kasance dandalin hadin gwiwar kasa da kasa, a maimakon fagen takara a tsakaninsu.”(Lubabatu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Tsokaci A Kan Karin Aure Cikin Sirri (II)

Next Post

Qatar 2022: Faransa Ta Sha Kashi A Hannun Argentina Inda Ta Yi Nasarar Cin Kofin Duniya

Related

Fasahar Shayi Ta Sin Ta Samar Da Kwanciyar Hankali Da Nishadi Ga ‘Yan Nijeriya
Daga Birnin Sin

Fasahar Shayi Ta Sin Ta Samar Da Kwanciyar Hankali Da Nishadi Ga ‘Yan Nijeriya

8 hours ago
Xi Jinping Ya Taya Murnar Bude Bikin Baje Kolin Kayayyaki Na Yammacin Sin
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Taya Murnar Bude Bikin Baje Kolin Kayayyaki Na Yammacin Sin

9 hours ago
Ruhin Yuan Longping Ya Ba Da Tabbaci Ga Samar Da Isashen Hatsi a Nahiyar Afirka
Daga Birnin Sin

Ruhin Yuan Longping Ya Ba Da Tabbaci Ga Samar Da Isashen Hatsi a Nahiyar Afirka

11 hours ago
An Kaddamar Da Babban Filin Wasan Da Kasar Sin Ta Gina Wa Kasar Chadi Kyauta
Daga Birnin Sin

An Kaddamar Da Babban Filin Wasan Da Kasar Sin Ta Gina Wa Kasar Chadi Kyauta

12 hours ago
Firaministan Sin Ya Sauka A Indonesia Domin Ziyarar Aiki
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Sauka A Indonesia Domin Ziyarar Aiki

1 day ago
Firaministan Sin Ya Shugabanci Taro Kan Masana’antu Masu Amfani Da Makamashi Mai Tsafta Da Kare Muhalli 
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Shugabanci Taro Kan Masana’antu Masu Amfani Da Makamashi Mai Tsafta Da Kare Muhalli 

1 day ago
Next Post
Qatar 2022: Faransa Ta Sha Kashi A Hannun Argentina Inda Ta Yi Nasarar Cin Kofin Duniya

Qatar 2022: Faransa Ta Sha Kashi A Hannun Argentina Inda Ta Yi Nasarar Cin Kofin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Ƴansanda Sun Bankaɗo Maɓoyar Ƴan Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Mutum 2

Ƴansanda Sun Bankaɗo Maɓoyar Ƴan Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Mutum 2

May 25, 2025
Fasahar Shayi Ta Sin Ta Samar Da Kwanciyar Hankali Da Nishadi Ga ‘Yan Nijeriya

Fasahar Shayi Ta Sin Ta Samar Da Kwanciyar Hankali Da Nishadi Ga ‘Yan Nijeriya

May 25, 2025
Chelsea, Man City, Newcastle Sun Samu Gurbi A Gasar Zakarun Turai Ta Baɗi

Chelsea, Man City, Newcastle Sun Samu Gurbi A Gasar Zakarun Turai Ta Baɗi

May 25, 2025
Xi Jinping Ya Taya Murnar Bude Bikin Baje Kolin Kayayyaki Na Yammacin Sin

Xi Jinping Ya Taya Murnar Bude Bikin Baje Kolin Kayayyaki Na Yammacin Sin

May 25, 2025
Dabarun Tinubu Sun Ƙara Kuɗaɗe A Harkar Ma’adanai Daga Naira Biliyan 6 Zuwa Biliyan 38 — Alake

Dabarun Tinubu Sun Ƙara Kuɗaɗe A Harkar Ma’adanai Daga Naira Biliyan 6 Zuwa Biliyan 38 — Alake

May 25, 2025
Fitaccen Fastan Kaduna Rabaran Azzaman Ya Mutu A Haɗarin Mota

Fitaccen Fastan Kaduna Rabaran Azzaman Ya Mutu A Haɗarin Mota

May 25, 2025
Ruhin Yuan Longping Ya Ba Da Tabbaci Ga Samar Da Isashen Hatsi a Nahiyar Afirka

Ruhin Yuan Longping Ya Ba Da Tabbaci Ga Samar Da Isashen Hatsi a Nahiyar Afirka

May 25, 2025
Gasar Wasanni Ta Kasa: Jihar Binuwai Ta Samu Kyaututtuka 9 Zuwa Yanzu

Gasar Wasanni Ta Kasa: Jihar Binuwai Ta Samu Kyaututtuka 9 Zuwa Yanzu

May 25, 2025
Tsadar Farashin Ƙwai Ya Sa Ƴan Nijeriya Sun Haƙura Da Cinsa

Tsadar Farashin Ƙwai Ya Sa Ƴan Nijeriya Sun Haƙura Da Cinsa

May 25, 2025
An Kaddamar Da Babban Filin Wasan Da Kasar Sin Ta Gina Wa Kasar Chadi Kyauta

An Kaddamar Da Babban Filin Wasan Da Kasar Sin Ta Gina Wa Kasar Chadi Kyauta

May 25, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.