Ci gaba daga makon jiya…
Yana daga alfanun bayyana wa uwargida matansu zancen karin aure da wuri ko dan ta shirya dakinta ta kuma saka a ranta cewar ta kusan zama ba ita kadai a gidan ba, ta san abubuwan da za ta kiyaye da wanda za ta rinka daga kafa ga miji da Amarya tun kafin zuwar Amarya, ba wai sai rana tsaka, ba tare da ta san komai na game da yadda ma ake tarbar Amarya ba, bata gyara kanta ta kimtsa ba, karshe a kawo mata Amarya dangin Amaryar da ‘yan unguwa da dangin miji na kallon uwargida a wulakance, a ballaganzance, kowa na fadar abin da ya zo bakinsa akan uwargida, wasu ma su ce bakin ciki ne ya sa taki gyara kanta da shirya dakinta da ‘ya’yanta, dan wani ma sai ranar da Amaryar za ta tare zai sanar mata, ko kuma ta jiyo a makwabta ko bakin ‘yan unguwa, wanda in aka buncika ita matar ko hanyar wajen malami ma ba ta sani ba bare kawayen banza masu hudubar tsiya. Ya kamata Maza masu irin wannan dabi’a su rinka tunawa da cewa; Duk abin da kai wa ‘yar wani kai ma za a yi wa taka ko ‘yar uwarka. Su ma mata su zamo masu hakuri da kuma daukar dangana a duk lokacin da miji ya sanar da su, a danne zuciya sosai a tausheta, kishi halak ne domin shi yake nuni da mace tana son mijinta amma a sassaita shi, domin su maza an halatta musu auran mata sama da daya, muddin za su iya adalci.
Ku ma maza masu irin waccen dabi’ar ta auren sirri ko auren boye zance ne gashi nan dai, ku kara gane cewa muddin za ku yi hakan alama ce ta rashin adalci, dan ita ma wadda ka auro za ka yi mata hakan a duk lokacin da wani karin auren ya zo zuciyarka. Wasu ba laifin mazan bane, laifin uwar miji ce idan ba ta san sirikar sai ta kulla hakan ta ce kuma.kar a sanar mata, shi kuma mijin dole ya bi, wasu kuma hakinsu ne yake jaho musu hakan, ya kamata a rinka sara ana duban bakin gatari.
Ga dai ci gaban ra’ayoyin ma’abota wannan shafi kan wannan lamari, kamar haka:
Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano:
Tsabar munafunci ne namiji in zai kara aure ba zai sanar da matarsa ba ranar da ake daurin aure ko ana igobe, wata ma sai dai ta ji a unguwa ko wajen kawarta ko wajen wasu dai, amma shi mijin bai sanar da ita ba sabida tsabar munafunci, sai ya ki fada wa matar wai dan kar su yi rigima, kuma hakan da yayi ba karamin ruguza gidansa yayi ba shi da kansa. Tunda ai namiji an bashi damar ya kara aure har sau uku muddin zai iya adalci, mene amfanin boyewar?
ba shi da wani amfani muddin ya isa da gidansa. Hakan yana haifar da tadhin hankaki ba kadan ba, tare da matsaloli masu yawa. Hanyar da za a magance matsalar guda 1 ce, namiji in zai kara aure ya sanar da matarsa kafin kowa ya ji ita ya kamata ta fara sani, duk wani bacin rai da za ta yi ai ba haramun bane, tunda kuwa kishi halitta ne dole ne mace tayi kishin mijinta muddin tana sonsa, Allah sa mu dace.
Aisha Sani Abdullahi daga Jihar Jos Marubuciyar Hausa:
Rashin gaskiya da son zuciya. Tabbas! ba abun da ke dawainiya da yawan maza a zamanin yanzu fiye da rashin gaskiya mai cike da son zuciya, mata na da hakkin sanin duk halin da mijinta ke ciki bare kuma batu na kara mata (abokiyar zama), a takaice zan iya yi wa wannan lamari da kallon cewa rashin daraja da martaba ‘Ya’ya mata da wasu mazan ke yi ne ya ke janyo hakan. Domin kuwa duk mai ganin darajar matarsa ba zai taba kai ta hanyar tozarci ba, bare har ya munafurce ta da yin auren karan tsaye. Ba zan gaza da furtawa ba kan ban da tsantsar son zuciya da rashin martaba mace ba abun da ke janyo hakan. Hanyar magance hakan kam ai babu ita, domin kuwa ba bin miji mace ke yi ba duk inda zai kasance da har za ta fahimci halin da yake ciki ko abun da yake shirin kullawa. Shawarar ba ta zarce kan su ji tsoron Allah ba, su tuna daraja, martaba da kuma hakkin matansu da ke wuyansu.
Khausar Salissou Ousmane daga Nijer/maradi:
Tabbas! mafi yawancin maza a yanzu idan za su kara aure ba sa sanar da matansu sai lokaci ya zo gaf, addini bai ce hakan ba Sam, wannan kam sabon yayi ne. Abin da ya jawo hakan a nawa ganin shi ne; wasu mazan na tsoron rigima ko tashin hankali da suke hangowa a gun uwayen gidansu, wasu ma suna ganin kamar matarsa ba za ta bar sa kara auren ba, ko kuwa dai sam! babu kwanciyar hankali tsakaninsu kuma laifin na uwar gidan ne to shi ne za ki samu irin hakan. Hakan kan kawo matsalar rashin jituwa tsakanin matan musanan man uwar gidan za ta ji babu wanda ta tsana a duniya irin matar kuma za ta rinka yi wa mijin kallon maci amana.
Hanyar da nake gani za a magance wannan matsalar shi ne; Dukkanmu mu ji tsoron Allah mu sakawa zuciyoyinmu cewa Aure bautar Allah ne, kuma sunnar Annabin Rahma ne SAW, mu zauna lafiya da juna dan mudin ana zaune klau hakan ba ta faru ba. Shawarar da zan ba mu baki daya shi ne; mu zauna lafiya mu so junanmu domin Allah, ayi hakuri da rayuwa, mu rinka yi wa juna adalci a zamantakewar yau da kullum, mazanmu kuma su daina yi mana irin wannan danyen kashin sam! ba adalci bane.
Bilkisu Musa Galadanchi Sokoton Nijeriya:
To a gaskiya wannan kuskure ne babba daga wurin maza, wanda baya bisa tsarin addini da kuma al’adar malam bahaushe. Hakki ne a gare ka ka sanarwa matarka akan karin auren da za ka yi ko don samun ingantaccen zaman lafiya. A gaskiya wannan matsalar tushenta mata ne. Mata sune tushen matsalar saboda tashin hankalin da suke yi wa mazajensu a duk sanda suka fara zancen karin aure. Matsaloli kam da dama, na farko rashin zaman lafiya tsakanin miji da mata, na biyu ita macen za ta dawwama tana ganin laifin miji, kuma zai iya kawo tsana a tsakanin matar da amaryar da aka auro.
Ta hanyar yi wa mata nasiha akan su daina dagawa mazajensu hankali idan sun yi zancen karin aure, su kwantar musu da hankali tare da yi musu addu’a shikenan in sha Allah. Mazan dake yin hakan ku ji tsoron Allah, ku sani hakan ba daidai bane, yanada kyau ku nemi wata hanya mafi sauki ku sanar da su akan yaudarar su, idan suka ji a bazata ba za su ji dadi ba.
Abba Abubakar Yakubu daga Jihar Jos:
BAI DACE MAZA SU RIKA BOYE WA MATANSU SHIRINSU NA KARA AURE BA; Darasin wannan makon mai matukar girgiza zuciya ne, saboda yadda irin wannan halayyar ta abokan mu ke rusa zaman lafiyar gidaje da haifar da rabuwar auratayya da dama. Babu shakka ana samun wannan hali daga wasu maza da ke ganin boyewa matansu na gida aniyar su ta kara aure, sai ana dab da daura auren ko bayan an daura ba abu ne mai dadi ba, musamman ga su matan da ke gida.
Suna daukar wannan abu a matsayin cin amana, yaudara, mugunta da munafurci, saboda boye musun da aka yi. A wajen wasu matan sanar da su wata za ta shigo gidanta a matsayin kishiya ko abokiyar zama yana ba ta damar nazartar yanayin da zaman ta zai kasance, shiryawa dakinta, don ka da wacce za ta shigo ta raina mata.
Haka kuma da dama mata na amfani da wannan damar ta sanin za a yi musu kishiya, don su yi bincike a kan wacce za ta shigo, halayyar ta da na iyayenta ko halin ‘yan gidansu, domin su san abin da zai iya biyo bayan sbigowarta gidan. A wajen wasu ma sani da wuri yana ba su damar shiga wajen malamai ko bokayensu a yi kulle kullen yadda za a bata shirin auren. Don haka sanarwa mace za a yi mata kishiya da wuri yana da muhimmanci a wajenta.
Kuma har wa yau girmamawa ce da mutuntawa, duk da yake babu macen da za ta yi murna da labarin kishiya, amma yana sa wasu natsuwa da shiga taitayinsu, don kyautata alakar su da mijinsu da kuma makomar yaran da suka haifa. Ko da yake ni ba malami ba ne, dalibi ne mai sauraron koyarwar malamai, na fahimci cewa, babu wajibci a kan namiji ya nemi izini ko amincewar matarsa kafin ya kara aure, amma hakkinta ne a sanar da ita, a matsayinta na wacce ake aure, kuma wacce za ta zauna da wacce za ta shigo. Ko da yake an samu sabani a kan haka, amma fahimta mafi rinjaye ita ce bayanin da aka yi na farko.
Don haka malamai ke karfafa muhimmancin biyayya ga umarnin Allah Madaukakin Sarki na zama da mata cikin kyautatawa da adalci. Ka da a zalunce su kuma ka da a tauye musu hakkinsu na zaman aure, wanda a ciki har da sanar da su a kan lokaci idan da akwai shirin kara aure.
Sau da dama abin da ke kawo wasu maza suke boyewa matansu za su kara aure shi ne fargabar abin da zai biyo baya, halayyar da za ta nuna idan ta samu labari, da gudun abin da za ta aikata saboda zafin kishi. Shi ya sa wasu ke jinkirta fadawa matansu halin da ake ciki, sai komai ya kankama, wasu ma sai sun yi auren har amaryar ta tare a wani waje sannan suke fadar abin da ya faru, ko kuma idan asiri ya tonu.
Kamar yadda yake da muhimmanci maza su rika samun hanyar sanar da matansu aniyarsu ta karin aure ko da kuwa za su nuna fushi ko bijirewa na rashin amincewa, haka su ma mata ya kamata su rika rage zafin kishi da bakaken maganganu, gorace gorace da cin mutuncin miji da danginsa, domin hakan shi yake kara bata tsakaninsu da mazajen da lalata zamantakewar auren. Har ma kuma wacce za ta shigo din ta samu kofar raina, wacce ta zo ta samu, saboda ta kasa daurewa zuciyar ta, da kawar da kanta.
Abdullahi Muhammad daga Jihar Kano Nassarawa Brigade Gama-A:
Abun da yasa maza ke boye karin aurensu ga matayensu shi ne; tsoron halin matayensu wanne mataki za su iya dauka idan suka ji haka, duk da hakan gaskiya bai dace ba ace sai ana gobe aure za ka sanar da matar ka. ba komai ne ya janyo haka ba illa su matan wasu kishinsu ya wuce na misali, domin wasu komai za su iya yi idan suka ji za a yi musu kishiya.
Eh toh! gaskiya matsala kam ana samun ta domin wata ma hakan zai iya yin sanadiyyar mutuwar aurenta musamman idan ta kasa jure wannan kaddara da ta same ta. Hanyar magance wannan lamari shi ne mutum ya tsaya ya san wace irin zafin kishi matar sa take da sannan sai ya san ta yadda zai bullo mata ya fada mata cikin lumana ba tare da tashin hankali ba. Masu yin haka kawai su ji tsoron Allah su kyautata niyyar su sai Allah ya taimake su, kar su yi auren domin hukunta uwar gida su yi auren dan Allah, sai ya taimake su.