A yau Talata ne ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira taron manema labarai, inda ya bayyana cewa, harkokin kasuwanci a sassan kasar na gudana cikin tsari yayin da ake tunkarar lokacin Bikin Bazara na kasar.
Kamar bukukuwan sallah da na kirismeti, Bikin Bazara gagarumin biki ne da Sinawa har ma da sauran wasu al’ummomi a fadin duniya ke murnarsa.
- Bikin Bazara Da Ke Fadada A Duniya Alama Ce Ta Mu’amala Da Fahimtar Juna Tsakanin Wayewar Kan Kasar Sin Da Wayewar Kai Daban-Daban
- An Gudanar Da Bukukuwan Shagalin Murnar Bikin Bazara Na CMG A Habasha Da Amurka Da Rasha
Abun da ya ja hankalina game da taron manema labaran na yau shi ne, yadda bayanai suka nuna cewa, farashin kayayyaki bai sauya ba sam, sabanin abun da na saba gani a lokacin karatowar bukukuwa a yankunanmu, wato tsawwalar farashin kayayyaki. Burin kasar har kullum shi ne, kyautatawa da saukakawa al’umma yanayin rayuwa. Gwamnati kan dauki matakan da suka dace na ganin al’ummarta ba su shiga cikin kunci ba, kuma ba kawai ana daukar matakan ne a fatar baki ba, a’a ana ganin kyawawan tasirinsu a aikace, kamar yadda ake gani a yanzu.
Abu na biyu shi ne, lokacin bukukuwan kan zo da karin bukatun kayayyaki da hidimomi, kuma a yayin taron manema labaran na yau an bayyana cewa, akwai isassun kayayyaki a kasuwannin sassan kasar. Wato baya ga tabbatar da rashin sauyawar farashi, an kuma tabbatar da wadatuwar kayayyakin. Sabanin yadda ’yan kasuwa kan boye kayayyaki domin kara farashinsu, sai na ji an ce an samar da karin kayayyaki har ma yawansu ya karu da kaso 10 zuwa 20 idan aka kwantanta da farkon shekara. Wannan wata kyakkyawar dabara ce ta tabbatar da al’ummar Sinawa sun gudanar da wannan kasaitaccen biki cikin farin ciki da kwanciyar hankali. A ko da yaushe na kan ce, duk wani kuntatawa da za a yi wa kamfanonin kasar Sin a kasashen waje, ba zai taba hana ci gaban tattalin arzikin kasar ba, saboda babbar kasuwar cikin gida da take da shi. Kasar Sin ta mayar da hankali wajen bunkasa tattalin arzikinta a cikin gida ta hanyar albarkar jama’a da ta mallaka. Misali, a wannan lokaci da Bikin Bazara ke karatowa, cinikayyar kayayyaki ta karu da kaso 19.9 a kan na watan Disamba. Haka a bangaren sufuri, inda ake sa ran za a yi kimanin tafiye biliyan 9 baya ga bangaren yawon bude ido dake samun tururuwar jama’a.
Nasarar dukkan wadannan abubuwa da na zayyana, ya samo asali ne daga kyakkyawan tsarin shugabanci irin na kasar Sin da kishin al’ummarta da muradin ganin ta kyautata musu rayuwa. (Fa’iza Mustapha)