Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Binicius Jnr, ya bayyana cewa gasar La liga da a baya aka santa da ‘yan wasa irinsu Ronaldinho da Ronaldo da Cristiano da Messi yanzu ta koma gasar masu nuna wariya a duniya.
Dan wasan ya bayyana haka ne bayan da magoya bayan Balencia suka dinga furta masa kalaman nuna wariya a wasan da Real madrid ta yi rashin nasara a hannun Balencia da ci 1-0 a gasar La liga da suka buga a ranar Lahadin da ta gabata.
Sai dai shima kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya ce La Liga tana da matsalar kalaman wariya, bayan da aka ci zarafin dan wasansa Binicius Junior a Balencia ranar Lahadin.
An bai wa dan kwallon na Brazil, mai shekara 22 jan kati a minti na 97, bayan cacar baki mai zafi da shi da Hugo Duro, sai dai tun farko an ja hankalin alkalin wasan, domin ya umarci magoya bayan Balencia su dakatar da kalaman wariya da suke yi wa dan kwallon Real Madrid din.
”Wannan abin da muka gani ba abin da za mu amince bane domin gabaki dayan filin wasa na rera kalaman wariya,” kamar yadda mai koyarwa Carlo Ancelotti ya sanar da jarisar Mobistar Plus.
Ya kara da cewa ”Bana son yin magana a kan kwallon kafa domin ba wani amfani a yi magana a kan ta kuma na sanar da alkalin wasan da ya kamata ya tsayar da karawar.”
Ya ci gaba da cewa La Liga tana tare da babbar matsala domin shi a wajensa Binicius dan kwallo ne mai mahimmaci a duniya saboda haka ya kamata a dakatar da wannan halayyar a lokacin wasanni.
Binicius, wanda karon farko kenan da aka yi masa jan kati a tarihinsa na kwallon kafa, ya fuskanci kalaman wariya da na cin zarafi karo da dama a La Liga a kakar nan kuma a wannan karon an dakatar da wasa a zagaye na biyu, bayan da dan kwallon ya nuna bacin ransa kan kalaman wariyar da ake rerawa.
Daga lokacin ne ransa ya baci har ta kai da aka yi masa jan kati a fafatawar da aka ci Real 1-0, karo na takwas da ta yi rashin nasara a La Liga a bana amma Balencia, wadda ta ci wasan ta yi sama zuwa ta 13 da tazarar maki biyar tsakaninta da ‘yan ukun karshen teburin La Liga.