Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ƙaryata zargin da a ke masa na cewa ya kashe sama da Naira Miliyan 400 a fannin tafiye-tafiyensa zuwa ƙasashen waje.
Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu ya bayyana wannan labari, wanda ya samo asali daga wata jaridar yanar gizo, a matsayin wani shirri da aka tsara da gangan don a ɗauke hankalin gwamnatin.
- Gwamnatin Kano Ta Mayar Da Daliban Borno Gida Bayan Kammala Karatunsu A Kano
- Za A Fuskanci Karancin Motoci A Nijeriya Sakamakon Karin Haraji
Kakakin Gwamnan ya bayyana cewa, “Wata jaridar yanar gizo ce ta kawo labarin wai Gwamna Lawal ya kashe N170,276,294.31 a fita ƙasar nan, sannan ya kashe N221,567,094 a tafiye-tafiyen cikin ƙasa, sannan ya kashe N6,929,500.00 a tsaro na musaman a cikin watanni uku.
Ya ce, wannan kuskuren fahimtar ya samo asali ne bisa murguɗe jadawalin kasafin kuɗi, alhali sun manta kashi na farko na shekara, na biyu da na uku, duk sun faɗo ne a gwamnatin da ta gabata.
Sanarwar ta Sulaiman, ta ce, “Mun ga wani rahoto da ya yi zargin cewa Gwamna Dauda Lawal ya kashe sama da Naira Miliya. 400 kan tafiye-tafiyen ƙasashen waje. Wannan ƙarya ce da nufin ci wa Gwamnan mutunci.”
Ya ci gaba da cewa, yin komai a bayyane, ita ce silar gwamnatin Dauda Lawal. Duk wani bayani da a ke nema, za a iya samu a manhajar gwamnatin ta yanar gizo a zamfara.gov.ng.
Yana mai cewa, su a wannan manhaja ta gwamnatin jihar, akwai cikakkun bayanai game da yadda gwamnatin ke tafiyar da kasafin ta, wanda kuma ke ƙunshe da abubuwan da Gwamnan ke kashewa a tafiye-tafiye dalla-dalla.
Ya ce, “A gwamnatin Dauda Lawal, muna da cikakken tsarin yin komai a bayyane, ta yadda babu wata kafa da za a yi almundahana da kuɗaɗen gwamnati.”
Da ya ke bayani game da tafiye-tafiyen da Gwamnan ya yi kuwa, Idris cewa ya yi tafiye-tafiyen aiki uku ne kawai Dauda Lawal ya yi tun da ya karɓi mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Ya ce, “Tafiye-tafiyen ayyuka uku da ya yi, su ne: Halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar Amurka; Wani taron ƙara wa juna sani na ƙungiyar ‘United Nations Development Programme (UNDP) a garin Kigali na ƙasa Ruwanda; da kuma taron da ya yi da Shugaban Bankin ci gaban Afrika, Dr Akinwumi A. Adesina a Abidjan ta ƙasar Kodebuwa.”
Ya ci gaba da bayyana cewa, “Bugu da ƙari, taron da ya halarta a Kigali, ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya ne ta shirya shi, sannan ƙungiyar ‘United Nations Development Programme (UNDP)’ ta ɗauki nauyin taron. Don haka babu ko kwabon da gwamnati ta kashe a kai. Inda aka kashe kuɗi a tafiye-tafiyen, biyu ne kawai na Majalisar Ɗinkin Duniya na Amerika da wanda Gwamnonin yankin Arewa maso Yamma suka gudanar da Shugaban bankin AfDB a Abidjan.”
Sanarwar ta ce, masu wancan labari, sun yi kuskuren ɗora kuɗaɗen da waccan gwamnatin ta kashe ne a kan gwamnatin mu. Babu inda Gwamnatin mu ta ɗauki wasu jami’an tsaron na kanta, ba su kuma yi wani watan Ramadan a kan mulki ba. Don haka mun kasa gane yadda aka jingina mana kuɗaɗen da aka kashe a watan Ramadana da na salla ƙarama.”
Ya ce, su a gwamnatin su, sun samu jajircewa wajen gudanar harkokin gwamnati a bayyane, a fili babu muna-muna. “Mun yi wa Zamfarawa alƙawarin kawo canji mai ma’ana, kuma a kan haka muka tsayu don cika allawari. Tsarin gwamnatin mu na ceto al’umma, cikakken tsari ne da ya shafi kowane fanni na gwamnati, babu wani murguɗaɗɗen labarin da zai kawo mana cikas,” in ji Kakakin Gwamnan.