Tsohon Ministan yada labarai a Nijeriya, Lai Muhammad, ya cewa labarun karya sun kusa halaka aurensa da matarsa tun ta kamun fara, Lai ya bayyana hakan lokacin da yake magana kan irin tasirin da labarun ƙarya ke da shi a kafafen sadarwa na zamani.
Wani labari ne ake yaɗawa kan ce wa “Wai ɗana Ali yana da Dala Biliyan 1.3 a cikin asusunsa, dan haka take so na amince mata a ce ita tana cikin wanda za su yi tassarrufi da kudin”.
- Hedikwatar Tsaron Nijeriya Ta Bayyana Sunayen ‘Yan ta’adda 97 Da Ake Nema Ruwa A-jallo
- Abu Bilal: Farfesan Da Ke Sana’ar Walda A Nijeriya
Ministan ya ce, ya sha wahala sosai kafin ta yarda cewa labarin nan ba gaskiya ba, labarin kanzon kurege ne kawai.
Yada labaran karya a shafukan sada zumunta ya zama ruwan dare a wannan lokacin, kuma lamarin kara gaba yake kamar wutar daji, shin ko wata hanya za a bi don magance wannan matsala.