Wasu ’yan ta’addan Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a ƙauyen Morai, da ke ƙaramar hukumar Augie a Jihar Kebbi.
Wani mazaunin yankin, Malam Ibrahim Augie, ya ce lamarin ya faru ne bayan da Lakurawa suka kai hari suka sace shanu.
- Kudaden Musanyar Kasashen Waje Da Sin Ta Adana Sun Kai Fiye Da Dala Tiriliyan 3.2 A Watanni 16 A Jere
- Sabon Tsarin Harajin Kwastam Na Amurka Ya Kwace ‘Yancin Sauran Kasashe
Bayan samun labari, ’yan sa-kai da dama suka fito domin ceto shanun tare da fatattakar ’yan ta’addan.
Sun samu nasarar ƙwato shanun, amma ba su san cewa mayaƙan sun lura da su ba.
Daga nan ne Lakurawan suka buɗe musu wuta, inda suka kashe 13 a cikinsu.
Lamarin ya ƙara tayar da hankali a Jihar Kebbi, duba da yadda hare-haren ’yan ta’adda ke ƙaruwa a yankunan Arewacin Nijeriya.
A baya, wata kotu a Nijeriya ta ayyana Lakurawa a matsayin ƙungiyar ’yan ta’adda domin bai wa hukumomin tsaro damar amfani da ƙarfi wajen yaƙar su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp