Wani sabon farmakin da sojojin Nijeriya suka kai tare da haɗin gwuiwar sashin Sojoji sama na atisayen Fansar Yamma ƙarƙashin rundunar Arewa Maso Yamma ta Farautar Mujiya, a kan ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa a Jihar Kebbi, ya tilasta wa ‘yan ta’addar janyewa sakamakon hare haren da Sojojin Nijeriya suka gudanar.
Wani mai rahoto kuma masanin yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X (da aka fi sani da Twitter) a daren Laraba.
Zagazola ya ce dakarun sama da na ƙasa sun haɗa kai wajen kai hari a sansanonin Lakurawa, wanda ya haifar da kwace dabbobi da sauran kayan abinci, waɗanda ke zama tushen hanyar samun kuɗin shiga ga ƙungiyar ta’addancin.
Sakamakon farmakin, ƙungiyar Lakurawa ta fara janyewa zuwa Borgu, wani yanki mai muhimmanci a kusa da iyakar Nijeriya da Benin a jihar Neja, wanda ke da hanyoyin samun kuɗin shiga ta hanyar dabbobi da kayan amfanin gona.
Ya ƙara da cewa, akwai yiwuwar ƙungiyar za ta ci gaba da tafiya kudu zuwa Ilesha Bariba a Jihar Kwara, kusa da iyakar Benin, inda za su iya tserewa daga tsauraran bincike.
Ana kuma ba da shawarar ga jami’an tsaro su sa ido a yankunan kasuwanni da mahimman hanyoyin ketarewa don daƙile sabbin hanyoyin da za su iya tallafa wa ayyukan Lakurawa.