Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato ya gudanar da taron zaman lafiya da masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Bokkos kan sabbin kashe-kashe a yankin.
Taron dai wani bangare ne na kokarin maido da zaman lafiya bayan hare-haren baya-bayan nan da aka kai yankin a ranar 16 ga watan Nuwamba.
- Xi Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Ilimi Karo Na 16 Na Cibiyoyin Kimiya Na Kasashe Masu Tasowa
- Uwargidan Shugaban Nijeriya Aisha Buhari Ta Garzaya Asibiti
Da yake jawabi a taron da aka gudanar a gidan gwamnati, Lalong ya fusata kan yadda shugabannin al’umma suka kasa gano wadanda suka aikata laifukan.
Ya ce gwamnati ta dauki matakin kawo karshen matsalolin tsaro a jihar.
A cewarsa, ya rage wa ’yan uwa su ma su nemi mafita mai dorewa don kawo karshen rikicin.
Ya ce babu dalilin da zai sa a kashe rayukan mutane yayin da ya yi kira ga manoma da su kai rahoton duk wani barnar da aka yi wa gonakinsu ga hukumomin da abin ya shafa.
Gwamnan yayin da yake kira ga mazauna yankin da su zauna lafiya da juna, ya ce zai ci gaba da tabbatar da adalci wajen gudanar da ayyukansa.
Ya jaddada cewa hukumomin da abin ya shafa na ci gaba da gudanar da bincike kan kashe-kashen domin gurfanar da wadanda suka aikata laifin tare da jaddada kudirin gwamnati na samar da dawwamammiyar mafita kan matsalolin tsaro da suka addabi jihar.