Matashin ɗan wasan gaban Barcelona, Lamine Yamal, ya amince ya tsawaita kwantiraginsa da ƙungiyar har zuwa shekarar 2030.
Wannan mataki zai tabbatar da cewa zai ci gaba da taka leda a Catalonia na tsawon shekaru masu zuwa.
- ECOWAS Za Ta Aika Kwamitin Sulhu Zuwa Ƙasashen AES
- Gwamnatin Tarayya Ta Maka MultiChoice A Kotu Kan Karin Kuɗin DSTV Da GOtv
Yamal, wanda tauraronsa ke haskawa a Barcelona, yana da burin ci gaba da zama a kulob ɗin tun daga yarintarsa.
A wannan kaka kaɗai, ɗan wasan ya jefa ƙwallaye 11 tare da taimakawa an ci 15 a cikin wasanni 36 da ya buga.
Wannan bajinta tasa Barcelona ke hanzarta tsawaita zamansa.
Wakilin ɗan wasan, Jorge Mendes, ne ya tabbatar da batun sabon kwantiragin, yana mai cewa, duba da yadda Yamal ke taka leda a halin yanzu, yana da muhimmanci ya ci gaba da kasancewa tare da Barcelona.
Ƙungiyoyi da dama sun nuna sha’awar ɗaukar Yamal, amma Barcelona ta dage cewa ba za ta bari ya bar ƙungiyar ba.
Sabuwar yarjejeniyar za ta ƙara masa ƙarin kuɗin shiga da kuma kariya daga ƙungiyoyin da ke zawarcinsa.
Yanzu dai abin jira shi ne ranar da ɗan wasan zai saka hannu kan sabon kwantiragin domin tabbatar da amincewarsa da ci gaba da taka leda a Camp Nou.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp