Matashin É—an wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya kafa tarihi yana da shekaru 17.
Yamal ya zama ɗan wasa mafi ƙarancin shekaru a tarihin Barcelona da ya buga wasanni 100 a ƙungiyar.
- Tinubu Ba Ya Tsoma Baki A Ayyukan EFCC – Olukoyede
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Aiki Kan Rigakafin Covid -19
A ranar Laraba, Barcelona ta karɓi baƙuncin Inter Milan a filin wasa na Luis Companys, inda Yamal ya zura ƙwallo ta farko da Barcelona ta ci, sannan ya buga wasansa na 100.
A tsawon wannan lokaci, Yamal ya lashe kofuna kamar La Liga, Copa del Rey, da Spanish Super Cup.
Yamal ya buga wasanni 100, ya jefa ƙwallaye 22 da taimakawa wajen jefa 33.
Ya kai wannan mataki ne bayan lashe Copa del Rey a wasan ƙarshe da Real Madrid a filin wasa na La Cartuja a Seville.
Yamal ya fara buga wasa a Barcelona a shekara ta 2023, inda ya fara a gasar La Liga a wasan da suka buga da Betis, yana da shekaru 15 da watanni tara a lokacin.
Tun daga wannan rana, ya ci gaba da kafa tarihi a ƙungiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp