Cibiyar Daƙile Cututtuka ta Ƙasa (NCDC), ta tabbatar da cewa mutane 717 sun kamu da cutar zazzaɓin Lassa, yayin da 138 suka rasu a faɗin jihohi 18 a 2025.
Wannan na ƙunshe ne cikin rahoton mako na 18 da cibiyar ta fitar, inda aka nuna cewa adadin mace-mace ya ƙaru zuwa kashi 19.2, idan aka kwatanta da kashi 18 da aka samu a daidai wannan lokaci a shekarar 2024.
- ASUU Ta Yi Barazanar Maka JAMB A Kotu Biyo Bayan Samun Mummunan Sakamako A UTME
- Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin
Jihohin Ondo, Bauchi da Taraba ne suka fi yawan masu ɗauke da cutar, inda suke da kashi 71 cikin 100 na duka waɗanda suka kamu da cutar.
Cutar ta ɓulla a kananan hukumomi 93, yayin da aka samu mace-mace a jihohi 15 da suka haɗa da Edo, Ebonyi da Filato.
NCDC ta ce mafi yawan waɗanda suka kamu da cutar na tsakanin shekaru 21 zuwa 30 ne, duk da cewa akwai waɗanda shekarunsu daga ɗaya zuwa 96 suka kamu.
Maza sun fi mata yawa wajen kamuwa da cutar.
Hukumar ta kuma tabbatar cewa ba a samu sababbin waɗanda suka kamu da cutar ba daga ma’aikatan lafiya ba a wannan makon.
Haka kuma, tsarin haɗin gwiwa na yaƙi da cutar zazzaɓin Lassa na ƙasa na ci gaba da aiki don tsara matakan daƙile yaɗuwar cutar.
NCDC ta gargaɗi al’umma cewa ko da yake an samu raguwar sabbin masu kamuwa da cutar, har yanzu akwai barazanar cutar musamman a jihohin da ke da yawan masu cutar.
Ta kuma buƙaci jama’a su riƙa kiyaye tsaftar muhalli, kai rahoton alamomin cutar da wuri, da kuma nisantar ɓeraye domin su ne ke yaɗa cutar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp