Wani kwararen lauya mai zaman kansa da ke a Jihar Kaduna, Barista Ibrahim Sahu Abubakar ya koka kan yadda ake ci gaba da samun jinkiri wajen yanke hukunci a kan shari’u da ke gaban wasu kotuna a fadin kasar nan.
Barista Sahu ya yi koken ne a hirarsa da LEADERSHIP HAUSA a Kaduna, inda ya ce, “Kamar yadda na sha fada kan jinkirin wajen abin da ya shafi gabatar da shari’a abubuwa ne da dama da ke janyo hakan”.
Ya kara da cewa, a wani lokacin kuma ita kanta shari’ar irin yanayinta ya kansa a samu jinkiri, ana samun jinkirin ne daga wurin kotun ko kuma daga bangaren alkalin saboda wasu dalilai da aka samu.
Sahu ya buga misali da cewa, idan ka duba ana samun shari’a a gaban kotu da za ta dauki lokaci, inda ya kara da cewa a wani lokacin kuma za ka ga wasu lauyoyin suna rubuta wa kotu wata bukata na ta daga masu karar da suka shigar a gabanta saboda wasu dalilai nasu ko dai za su yi tafiya ko bin wata shari’ar da ya gabatar a gaban wata kotun ko kuma an yi masa rasuwa, ka ga wadannan dalilai ne da kotun za ta duba su.
Sahu ya bayyana cewa, a wani lokacin kuma neman shaidun da za gabatar a gaban kotu don su bayar da shaida idan ana yin wata shari’a, hakan kan zama wani babban aiki, inda za ka hakan na janyo ai ta dage shari’ar.
Lauyan ya sanar da cewa, yawan daukaka kara daga wata kotun zuwa wata hakan ma zai iya shafar shari’ar ta yi tsawo, inda ya kara da cewa, akwai kuma rashin yawan wadatattun kotuna alhali ga shari’oi da dama a gaban alakali.