Lauyoyi biyu, Ahmed Musa da Ridwan Yunusa, sun nesanta kansu daga wata ƙorafi da aka kai wa babban maga takardar kotun Jihar Kano domin gurfanar da mawallafin jaridar DAILY NIGERIAN, Jaafar Jaafar, da abokin aikinsa Umar Audu. Lauyoyin sun bayyana cewa sunayensu an saka su cikin jerin masu ƙara ba tare da yardarsu ba, abin da suka kira babban cin zarafi ga aikin lauya.
Rahotanni sun nuna cewa lauyan Gwamna Abba Kabir Yusuf, Hamza Nuhu Dantani na daga Potent Attorneys, shi ne ya shigar da ƙarar a madadin Abdullahi Rogo, Daraktan Kula da Al’amuran Bako na Fadar Gwamnatin Kano. Wannan ya biyo bayan wani rahoto da DAILY NIGERIAN ta wallafa, inda aka bayyana yadda ICPC da EFCC suka gano Rogo da hannu a satar Naira biliyan 6.5 daga asusun gwamnati zuwa asusun ’yan canji a Abuja.
- Mele Kyari Ya Bayyana A Ofishin EFCC Kan Zargin Badaƙalar Dala Biliyan 7.2
- EFCC, ICPC Sun Kwato Naira Biliyan 277.69 Da Dala Miliyan 106 A Shekara Guda
A cikin ƙorafin da aka sanya wa hannu a ranar 27 ga watan Agusta, Rogo ya yi iƙirarin cewa rahoton ya bata masa suna da kuma na iya haddasa rikici a cikin al’umma. Sai dai daga cikin jerin lauyoyin da aka ce sun sanya hannu, Musa da Yunusa sun yi watsi da hakan, inda suka ce ba su da hannu kwata-kwata a lamarin. Yunusa ya bayyana cikin sanarwa cewa ba ya tare da ofishin Potent Attorneys, kuma bai taɓa amincewa a yi amfani da sunansa ba.
Haka kuma Musa ya tabbatar da cewa sai da Yunusa ya sanar da shi aka haɗa sunansa cikin takardar ƙorafin. Ya ce duk da ya san wasu daga cikin lauyoyin da aka ambata, amma an ƙara nasa sunan ba tare da ya sani ba.
Wannan ya sake jefa shakku kan yadda ake amfani da dokoki wajen ƙaƙabawa ƴan jarida shari’ar batanci domin toshe bakin kafafen yaɗa labarai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp