Ƙungiyar lauyoyi mai suna “Lauyoyi masu kare dimokuraɗiyya” ta bayyana cewa tana ganin tsohon Shugaban NNPC Mele Kyari ya kasance “mai gaskiya” a lokacin da yake shugaban Kamfanin, inda ta yi tir da binciken da EFCC ke yi a kansa.
A wata sanarwa a ranar Litinin, ƙungiyar ta ce binciken na nuna alamar “ƙoƙarin bata sunan” Kyari, wanda ya jagoranci sauya NNPC zuwa kamfani kuma ya aiwatar da sauye-sauye masu mahimmanci a cikin masana’antar mai.
- Bayan Fara Binciken $2.96bn, An Samu N80bn A Asusun Tsohon Daraktan Kamfanin NNPCL
- Tinubu Ya Kori Mele Kyari, Ya Naɗa Ojulari A Matsayin Shugaban NNPC
“Kyari ya yi aiki cikin aminci daga 2019 zuwa 2025 kuma ya kawo sauye-sauye da suka haifar da cire tallafin man fetur da kuma haɓaka yawan aikin hakar mai,”
in ji Barrister Ndu Edede na ƙungiyar.
EFCC ta fara binciken ne bisa wata wasika da ta aika wa NNPC a ranar 28 ga Afrilu, inda ta lissafta Kyari da wasu tsofaffin jami’ai 14 a matsayin waɗanda ake bincika. Duk da haka, ƙungiyar lauyoyi ta ce binciken ya kamata ya kasance cikin gaskiya kuma ba tare da nuna son rai ba.
Har yanzu EFCC ba ta fitar da wani bayani na yadda binciken ke tafiya ba. Ƙungiyar ta kammala da cewa: “Duk wani bincike mai gaskiya zai nuna cewa Kyari ya yi aiki da gaskiya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp