• English
  • Business News
Saturday, October 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Layin Dogo Na Habasha Zuwa Djibouti Na Kara Habaka Hada Hadar Sufuri A Yankin Kahon Afirka

by CMG Hausa
2 years ago
Habasha

Layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti da kasar Sin ta gina, ya fara jigilar motocin daukar kaya a jiya Laraba, daga tashoshin ruwan Djibouti, zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Kashin farko na motocin 63 sun isa tashar Indode dake wajen birnin Addis Ababa a jiya Laraba, kuma ministan kula da sufuri da jigila na Habasha Denge Boru, ya bayyana lamarin a matsayin muhimmin ci gaba ga yunkurin Habasha na inganta bangaren sufuri da jigila.

  • Xi Ya Bukaci A Hada Hannu Wajen Gina BRI Domin Samar Da Sabbin Damarmaki Ga Hadin Gwiwar Asiya Da Turai

A hakika, tun bayan kaddamar da layin dogo na sufurin hajoji da jama’a, wanda ya hada kasar Habasha maras iyaka da teku da kasar Djibouti a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2018, yau sama da shekaru biyar, layin dogon na ta kara samun tagomashi, ta fannin bunkasa hada hadar sufuri, da kasuwanci tsakanin kasashen biyu, da ma kasashen dake shiyyar ta kahon Afirka.

Karkashin wannan katafaren aiki na ginin layin dogo da kasar Sin ya kammala tun a shekarar 2017, yanzu haka kasar Habasha ta samu babbar damar shigarwa, da fitar da manyan hajoji ta tashoshin jiragen ruwan na Djibouti. Har ma wasu alkaluma sun shaida yadda kaso sama da 95 bisa dari, na hajojin cinikayyar kasar Habasha ke bi ta tashoshin ruwan Djibouti.

Ko shakka babu wannan babban ci gaba ne a tarihin yankin kahon Afirka.

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya

Muna iya gani daga sakamakon ci gaban da layin dogon ya haifar, cewa baya ga saukaka safarar hajoji, jiragen kasa dake bin layin dogon, sun kuma saukaka sufurin fasinjoji, ta hanyar rage farashin zirga zirga tsakanin sassan kasashen biyu.

Irin wadannan nasarori da layin dogon ke samu, sun tabbatar da burin da kasar Sin tare da abokan huldar ta na nahiyar Afirka ke fatan cimmawa, ta fuskar gudanar da hadin gwiwa mai dorewa, wanda ke ingiza ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummun kasashe masu tasowa.

Ko shakka ba bu layin dogo na Habasha zuwa Djibouti, na ci gaba da bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu, da ma sauran kasashen yankin kahon Afirka, ta fuskar saukaka farashi, da lokacin safarar hajoji, baya ga kara inganta yanayin sufuri, da samar da karin guraben ayyukan yi ga al’ummun kasashen yankin, matakin da masharhanta ke ganin zai ci gaba da fadada cinikayya, da hada hadar shige da fice tsakanin kasashen yankin gabashin Afirka baki daya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 10, 2025
Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya
Daga Birnin Sin

Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya

October 10, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa
Daga Birnin Sin

CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa

October 10, 2025
Next Post
Awanni 24 Kafin Rantsarwa, Shugaban Rikon Kwarya A Jihar Yobe Ya Rasu

Awanni 24 Kafin Rantsarwa, Shugaban Rikon Kwarya A Jihar Yobe Ya Rasu

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya

Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya

October 11, 2025
Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano

Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano

October 11, 2025
Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

October 11, 2025
Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara

Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara

October 11, 2025
sallah

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida

October 11, 2025
Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 10, 2025
A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho

October 10, 2025
Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya

Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya

October 10, 2025
peter

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

October 10, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa

CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.