Dabbobin da ake layya da su, su ne tumaki da awaki da shanu da raƙuma. Duba Alma’ūnatu [1/484] da Aƙrabus Sãliki [shafi na 47] da Assamarud Dãnī [ shafi na 390-391] da Almuntaƙã Sharhul Muwaɗɗã [4/160]
Ana yin layya da tumaki idan suka cika shekara ɗaya suna harin shiga ta biyu koda da ‘yan kwanaki ne. Awaki kuma waɗanda suka cika sheka biyu ko kuma suna cika shekara ɗaya suna harin shiga ta biyu ko da wata ɗaya ne. Shanu kuma ana layya da su, idan suka cika shekara uku ko suka shiga ta huɗu, raƙuma kuma waɗanda suka cika shekara biyar ko suka shiga ta shida. Duba; Attaju Wal Iklil [4/463] Sharhus Sagīr [2/339] Masãlikul Jalãlati [2/822] da Assamarud Dãnī [ shafi na 390-391]
Za a iya layya da tumaki waɗanda suka cika wata shida zuwa goma mafi ƙaraci. Duba; Alkãfi [shafi na 237-238] da Alma’ūnatu [1/486]
Ana ganin shanun da suka cika shekara biyu ko suka shiga ta uku za a iya layya da su. Alkãfi [shafi na 238] da Alma’ūnatu [ 1/486].
Raƙumi idan ya cika shekara biyar ko ya shiga ta shida koda da rana ɗaya ne za a iya layya da shi. Sirãjus Sãliki [2/12] da Alkãfi [238].
Duk dabbar da bata cika waɗannan shekaru da aka ambata ba, to bai halatta a yi layya da ita ba, idan kuma an yi da ita to layyar bata yi ba. Almudawwanatul Kubrã [1/610].
A Malikiyya yin layya da tumaki ta fi falala, sa’n nan shanu sai kuma raƙuma. Duba; Attalƙīnu [ shafi 211] da Aƙrabus Sãliki [ shafi na 47].
Rago mai fari da baƙi mai manyan ƙaho ya fi kowanne falala a wajen layya a Mazhabar Malikiyya. Duba; Almuƙaddimut Muhimmãt [1/336]
A guji sayen dabbobin da ba su isa layya ba musamman shanu da raƙuma, domin ibada ana yinta ne da abin da Allah ya shar’anta.
Mu haɗu a rubutu na uku don sanin sifofin dabbar layya.
Nuhu Ubale Ibrahim
(ABU RAZINA PAKI)
8/12/1442
Bugu na biyu