A ranar Talata, 25 ga Fabrairu, 2025, jaridar LEADERSHIP ta gudanar da bikin karrama waɗanda suka lashe gasar rubuta gajerun labaran soyayya ta Hausa ta hanyar kiran bidiyo na WhatsApp. Wannan gasa an shirya ta ne domin ƙarfafa gwuiwar masu bibiyar LEADERSHIP HAUSA tare da bunƙasa fasahar rubutu a cikin al’ummar masu magana da Hausa.
Taron ya samu halartar jagororin LEADERSHIP, ciki har da Shugaban Sashen Dijital, Mista Samuel Ossai, Editan LEADERSHIP HAUSA, Malam Bello Hamza, Shugaban Sashen LEADERSHIP HAUSA Online, Muhammad Bashir Amin, da kuma Manajan Soshiyal Midiya, Malam Naziru Adam Ibrahim.
- Wakilin LEADERSHIP Ya Zama Shugaban Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai A Kebbi
- Tinubu Ya Taya Babban Editan LEADERSHIP, Ishiekwene Murnar Cika Shekaru 60
Gasar ta bayar da kyaututtuka na kudi ga waɗanda suka yi nasara: ₦50,000 ga wanda ya zo na farko, ₦25,000 ga wanda ya zo na biyu, da ₦10,000 ga wanda ya zo na uku. Alƙalan gasar, ƙarƙashin jagorancin Muhammad Bashir Amin, sun tantance labarai bisa la’akari da ƙirƙira, asali, da kuma ingancin labari.
A jawabinsa, Editan LEADERSHIP HAUSA, Malam Bello Hamza, ya taya dukkan mahalartan murna tare da karfafa musu gwuiwa kan ci gaba da bibiyar dandalin LEADERSHIP HAUSA. Haka nan, Shugaban Sashen Dijital, Mista Samuel Ossai, ya yaba wa alƙalan gasar da waɗanda suka yi nasara.
Zainab Muhammad, wacce ta zo ta biyu, ta yi jawabi a madadin masu nasarar, inda ta nuna godiyarta ga LEADERSHIP HAUSA bisa wannan dama da suka samu, tare da alƙawarin ci gaba da tallafa wa jaridar a shirye-shiryenta.
Waɗanda Suka Yi Nasara
1. Aliyu Usman Adam – Matsayi na Ɗaya
Aliyu Usman Adam, ɗan asalin Zariya, Jihar Kaduna, an haife shi a shekarar 1984. Ya kammala karatunsa na firamare da sakandare a Zariya, sannan ya samu digiri a harshen Hausa daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, a 2008. Bayan hidimar ƙasa a Jihar Edo, ya yi aiki a kamfanin SAN Yoghurt da kuma Alhuda Center School daga 2011 zuwa 2014.
A 2014, Aliyu ya koma aikin jarida, inda ya yi aiki da jaridar RARIYA a Abuja har zuwa 2017. A halin yanzu, shi ne Manajan shirye-shirye (Content Manager) a Nishadi TV Abuja. Yana da mata da ‘ya’ya biyu.
2. Zainab Muhammad (Indian Girl) – Matsayi Na Biyu
Zainab Muhammad, wacce aka fi sani da “Indian Girl,” ‘yar asalin ƙaramar hukumar Dala ce a Kano. Ta kammala firamare da sakandare a Kano, tare da burin ci gaba da karatun jami’a a nan gaba.
Zainab tana da ƙwazo a ɓangaren ilimin addinin Musulunci, kuma tana amfani da kafafen sada zumunta wajen ilmantarwa da faɗakarwa. A halin yanzu tana da tarin masoya saboda rubuce-rubucenta masu ƙayatarwa da gina al’umma.
3. Mujaheed Nuhu Yusuf (Mujaheed Matashi) – Matsayi Na Uku
Mujaheed Nuhu Yusuf, wanda aka fi sani da Mujaheed Matashin marubuci ne a fagen wasan kwaikwayo kuma mawaki daga Kano. Ya wallafa littattafai biyu na waƙoƙi, ciki har da Philosophy Mysterious Pen, wanda ya wallafa tare da marubuci Haiman Ra’ees.
Mujaheed shi ne shugaban ƙungiyar marubuta Ruhin Adabi, kuma yana wallafa rubuce-rubucensa a shirin Bakandamiya Hikaya da kuma shafinsa na Facebook.
Wannan gasa ta ƙara tabbatar da aniyar LEADERSHIP HAUSA na bunƙasa haɗaka da ƙirƙirar rubutu a cikin al’ummar Hausawa.
Jaridar na shirin ci gaba da shirya irin waɗannan gasar domin ƙarfafa sha’awar adabi da kuma ƙarfafa dangantaka da masu karatu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp