Hukumar gudanarwar jaridar LEADERSHIP, ta ce, bayan dogon muhawara da tattaunawa da hukumar yaki da ta’anmali da miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) tare da masu ruwa da tsaki, an kai ga daukar matakin dage taron da aka shirya kan illoli ta’anmuli da miyagun kwayoyi zuwa wani lokaci nan kusa.
“Muna cike da godiya da irin goyon baya da amincewa da abokan huldarmu da masu ruwa da tsaki suka yi,” a cewar sanarwar.
- Ribadu Zai Shugabanci Taron LEADERSHIP Da NDLEA Kan Yaki Da Miyagun Kwayoyi
- Yaki Da Miyagun Kwayoyi: Kamfanin LEADERSHIP Da NDLEA Sun Kulla Kawance
“Mun kai ga cimma matsayar dage wannan babban muhimmin taron zuwa wani lokaci, wanda za a sanar nan kusa kadan.”
Sanarwar ta kamfanin buga jaridun LEADERSHIP ta nuna damuwa kan duk wani ko wasu da wannan dage taron ya shafa musamman wadanda hakan bai musu dadi ba, tare da bada tabbacin cewa dagewar zai ba da dama a kara shirya taron da tsare-tsaren masu nagarta da za a kara a kan tsarin da aka yi tun farko.
LEADERSHIP, da hadin guiwar NDLEA ta amince da shirya babban taro da za a baje kolin illoli da hatsarorin da suke tattare da ta’anmuli da miyagun kwayoyi da yadda ke tasiri ga ta’addanci ga ci gaban gasa, tare da muhawara kan hanyoyin shawo kan matsalar.
A cewar binciken da majalisar dinkin duniya ta yi kan amfani da Miyagun Kwayoyi a shekarar 2017, kan kididdigar adadin ‘yan Nijeriya miliyan 98, mutum miliyan 14.3 su na ta’anmuli da haramtattun Kwayoyi ko masu illla.
Baya ga shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa (mai ritaya), babban mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu; fitacce kuma gogaggen lauya kan kare hakkin bil-adama, Mr. Femi Falana, SAN, da wasu shahararru duk sun amince kan cewa za su halarci taron har ma su gabatar da jawabai duk don neman hanyoyin dakile ta’anmuli da Miyagun Kwayoyi a Nijeriya.