Firaministan Li Keqiang ya gana da shugaban majalisar kungiyar EU Charles Michel a nan Beijing da yammacin jiya Alhamis. Michel ya sake nuna alhininsa game da rasuwar tsohon shugaban kasar Sin Jiang Zemin.
Li Keqiang ya bayyana cewa, muna matukar juyayin Jiang Zemin, kuma muna mika godiyarmu ga ta’aziyar da bangaren Turai ya yi wa bangaren Sin.
Li Keqiang ya bayyana cewa, Sin ta Turai suna taka babbar rawa wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaba a duniya, ka yi shawarwari mai zurfi da shugaban Xi Jinping. Bangaren Sin na son fadada hadin gwiwa da daidaita bambance-bambance ta hanyar da ta dace, da tabbatar da tsaron makamashi da abinci da tsarin samar da kayayyaki da jigilarsu tsakanin kasa da kasa bisa tushen mutunta juna, ta yadda za a sa kaimi ga bunkasuwar huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Turai.
Bangaren Sin yana tsayawa tsayin daka kan manufar goyon bayan cudanyar tattalin arzikin Turai. Ana fatan Sin da Turai za su kara bude kofa ga juna.
A nasa bangaren, Michel ya bayyana cewa, Tarayyar Turai tana tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, kuma tana fatan za a gudanar da sabon zagaye na ganawa tsakanin shugabannin Tarayyar Turai da Sin yadda ya kamata. (Safiyah Ma)