Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce ya kamata kasashen Sin da Jamus su yi aiki tare, wajen zurfafa hadin gwiwar raya tattalin arziki da fasahohi, ta yadda hakan zai zama wani misali, da jagoranci, a fannin karfafa hadin gwiwar cimma moriya tare tsakanin Sin da Turai, da ingiza ci gaban duniya.
Firaminista Li Qiang ya yi kiran ne a jiya Talata, yayin da yake halartar taron raya hadin gwiwar tattalin arziki da fasahohi tsakanin Sin da Jamus, karo na 11 a kasar Jamus.
Li ya kara da cewa, a wannan gaba da ake fuskantar sauye sauye, da rashin tabbas a duniya, karfafa hadin gwiwa zai taimakawa wajen cimma moriyar juna, da samar da kyakkyawan sakamako ga kowa, kana matakin shi ne ya dace a kara maida hankali a kansa.
Daga nan sai ya jaddada wajibcin mayar da batun hadin gwiwar raya tattalin arziki da fasahohi tsakanin sassan biyu, a matsayin muhimmin jigo na hadin gwiwar kasa da kasa, da rungumar matakan dunkulewar tattalin arzikin duniya, da goyon bayan cinikayya maras shinge, da bunkasa matakan cin gajiya tare, da habaka ci gaban bil adama.
A nasa bangare, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, cewa ya yi kasar ba za ta amince da manufofin raba kan kasashen duniya ba, za ta kuma nacewa aiwatar da matakai a bude, tare da karfafa hadin gwiwa tare da Sin, da gaggauta bunkasa hadin gwiwar sassan kasa da kasa bayan annobar COVID-19.
Scholz ya ce, Jamus a shirye take ta yi tukuru, wajen warware matsalolin hadin gwiwa ta hanyar tattaunawa, da gudanar da shawarwari tare da bangaren Sin. (Saminu Alhassan)