Yau Juma’a firaministan kasar Sin Li Qiang ya aike da sako ga Maria Benvinda Levy, don taya ta murnar hawan mukamin firaministar kasar Mozambique.
A cikin sakon, Li Qiang ya bayyana cewa, kasashen Sin da Mozambique na da dangantakar abokantaka na dogon tarihi, kuma zumuncin dake tsakanin kasashen biyu ya jure jarrabawa daga sauye-sauyen yanayin duniya, kuma abu ne da Hausawa ke cewa, Mahdi ka ture.
Li Qiang ya kara da cewa, a bana ake cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, kuma yana fatan yin aiki tare da firaminista Levy, don gaggauta tabbatar da matakan kawance guda goma da aka gabatar a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, kana da karfafa hadin kai a tsakanin kasashen biyu kan manyan tsare-tsaren samun ci gaba, da neman hadin gwiwa da samun bunkasuwa tare, ta yadda za a inganta dangantakar abokantaka irin ta hadin gwiwa a dukkan fannoni a tsakanin kasashen biyu kan kara samun nasarori masu yawa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp