Firaministan Sin Li Qiang, ya yi kira ga kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu, da su dauki juna a matsayin abokan tafiya, kuma damammaki na raya kai, da ingiza dunkulewar tattalin arzikin duniya, da cinikayyar maras shinge.
Li ya yi wannan kira ne a jiya Lahadi, yayin da ya halarci taron shugabannin Sin da Japan da Koriya ta Kudu karo na 9 a Seoul fadar mulkin kasar Koriya ta Kudu.
Kaza lika a jawabin da ya gabatar, ya ja hankalin sassan da su bayyana adawar su ga mayar da batun cinikayya zuwa harkar siyasa, ko wasu batutuwa na tsaro, kana su yi watsi da kariyar cinikayya, da raba-gari, ko katse hada hadar shigar da hajojin sassan duniya. (Saminu Alhassan)