A yau Alhamis 4 ga watan Disamba da rana, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a nan birnin Beijing.
Li Qiang ya ce, kasashen Sin da Faransa dukkansu manyan kasashe ne masu karfin tattalin arziki a duniya, kuma mambobi ne na dindindin a kwamitin sulhu na MDD. Kiyaye ci gaba da sadarwa a kusa da juna, da daukar matakan daidaitawa, da aiwatar da ayyuka masu karfi, ba wai kawai za su samar da kyakkyawan yanayi na ci gaban bangarorin biyu a tare ba ne, har ma da sanya karin kwanciyar hankali da tabbaci a duniyar yau mai cike da fuskantar sauye-sauye masu nasaba da juna.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana da muradin yin aiki tare da Faransa don ci gaba da kokarin da take yi, da ci gaba da sada dadadden zumuncinsu, da karfafa amincewa da juna a fannin siyasa, da inganta hadin gwiwa a dukkan fannoni, da yaukaka alakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Faransa zuwa wani sabon mataki.
A nasa bangaren, Macron ya bayyana cewa, Faransa na da muradin inganta mu’amala da tattaunawa a dukkan matakai tare da kasar Sin, da kara bude kofa ga kasashen biyu, da zuba jari a tsakaninsu, da zurfafa hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya, da aikin gona, da fasahar sararin samaniya, da zirga-zirgar jiragen sama, da makamashin nukiliya na amfanin farar hula, da sabbin makamashi da dai sauran fannoni, da kuma yin nazari tare wajen lalubo karin kasuwa ga kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














