Jakadan kasar Sin game da kwance damar yaki Li Song ya ce, tutanin sake dawo da cacar baka, zai haifar da tarnaki ga bukatar da ake da ita, ta wanzar da ci gaba da daidaito a duniya baki daya.
Li Song wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, yayin taron mahawarar kwamitin farko na zaman MDD karo 77, wanda ya gudana a jiya Litinin, ya ce a yanzu haka tsarin tsaron duniya, da na lura da makamai, da na kwance damara, da hana bazuwar makamai na fuskantar kalubale tun bayan yakin cacar baka.
Jami’in ya kara da cewa, wasu kasashen dake da tunani irin na sake komawa cacar baka, na ci gaba da ingiza takara, da fito na fito tsakanin manyan kasashen duniya, suna karfafa rukunin kawancen sojinsu, tare da rura wutar kiyayya da sabani.
To sai dai Li ya ce, kasar Sin a nata bangare, tana shawartar manyan kasashen duniya, musamman masu mallakar makaman kare dangi, da su yi watsi da duk wani mataki na mayar da wasu saniyar ware, ko killace kai a fannin samar da tsaro, su kuma kaucewa daukar tsaron kansu sama da na sauran sassa. (Saminu Alhassan)