Wakilin dindindin na ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), kana darektan kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiyar JKS Li Xi, ya jagoranci tawagarsa don ziyarar aiki a kasar Afirka ta kudu bisa gayyatar da aka yi masa, daga ran 5 zuwa 7 ga watan nan da muke ciki. Yayin ziyarar, Li Xi ya gana da shugaban kasar, kana shugaban jam’iyyar ANC ta kasar Matamela Cyril Ramaphosa a Cape Town, da shugaban majalisar dokokin kasar, kana babban jami’i mai jan ragamar jam’iyyar ANC Thoko Didiza a Pretoria, da kuma babban darektan ANC, Fikile Mbalula.
Yayin ganawarsa da Ramaphosa, Li ya ce, Sin da Afirka ta Kudu na da dadadden zumunci, kuma a shekarun nan na baya, huldar kasashen biyu ta kara habaka karkashin jagorancin shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa Ramaphosa. Ya ce Sin na fatan kara hadin kai da kasashe masu tasowa don tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da ma inganta tushen amincewa da juna a siyasance da gaggauta hadin gwiwar tsare-tsaren raya kasashen biyu, da ma daga matsayin hadin kai da na cin moriya tare, da kara azama wajen tabbatar da ci gaban da aka samu a taron koli na Beijing na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka, kana da raya shawarar “ziri daya da hanya daya” mai inganci, da kuma daga huldar kasashen biyu zuwa wani sabon mataki. Ya kara da cewa, Sin za ta nuna wa Afirka ta Kudu cikakken goyon baya don ta zama kasar da za ta karbi shugabancin G20 a shekarar 2025, ta yadda za ta kara hadin gwiwa da kasashe masu tasowa da gaggauta ci gaban harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, ta yadda za a jagoranci sha’anin raya kasashe masu tasowa da masu saurin ci gaba baki daya da ma raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya. (Amina Xu)