Libiya ta ci gaba da kasancewa ƙasar da ke da farashin man fetur mafi arha a Afrika, inda farashin lita ɗaya na man yake 0.15 Libyan Dinar, wanda ke daidai da kusan dala $0.032 ko kuma ₦52 har a ranar 16 ga Satumba, 2024, kamar yadda Masu bibiyar farashin mai a duniya (Global Petrol Prices) suka ruwaito.
GPP, wata cibiyar da ke bibiyar farashin man fetur a duniya, ta nuna banbanci mai yawa na farashin man fetur a ƙasashen Afrika. Duk da cewa Libiya tana more mafi arha farashi, ƙasashe kamar Masar, Aljeriya, da Angola suna fuskantar farashi mafi tsada, inda farashin ya kai dala $0.279, $0.342, da $0.351 kowace lita.
- Sin Tana Fatan Bangarori Daban Daban Na Kasar Libya Za Su Sulhunta Ta Hanyar Yin Shawarwari
- An Kwaso ‘Yan Nijeriya 167 Da Suka Makale A Libya – NEMA
A gefe guda, farashin man fetur a Nijeriya ya tashi zuwa N1,000 kowanne lita, yayin da farashin a kasuwar bayan-fage ya kai har N1,600 kowanne lita. Duk da kasancewa mai samar da man fetur, hauhawar farashin man a Najeriya ya haifar da rashin jin daɗin jama’a, musamman bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin kasar ta yi.
Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ce ke da mafi tsadar man fetur a Afrika, inda farashin ya kai $1.83 kowanne lita. Sauran ƙasashen da ke da farashi mai tsada sun haɗa da Senegal ($1.646), Seychelles ($1.595), Zimbabwe ($1.590), Morocco ($1.527), Uganda ($1.475), da Kenya ($1.453).