Gwamnatin hadin kan kasa ta Libya ta amince bututun iskar gas na Nijeriya ya bi ta Kasarta zuwa Turai.
A cewar ministan mai da iskar gas na Libya, Mohammed Aoun, ya ce Nijeriya za ta samu ragowar Kilomita 1,000 idan ta bi ta kasar Libya maimakon ratsawa ta Kasar Algeria da Morocco zuwa kasuwannin turai, hakan zai rage farashin iskar gas da kuma na sufuri.
Sai dai Libya na fuskantar kalubale da dama don cimma wannan aiki; daga tsaro, kudi, fasaha da kalubalen kasuwanni a Duniya.
A cikin watan Yunin da ya gabata ne aka sanar da shirin fara aikin bututun iskar gas na Nijeriya zuwa kasar Libya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp