Kungiyar likitocin Nijeriya NARD a ranar Lahadi ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da ta shiga.
Shugaban kungiyar, Orji Emeka Innocent, ya shaida wa Daily Trust a daren jiya Lahadi cewa za a koma aiki da karfe 8 na safiyar yau Litinin 22 ga watan Mayu.
Kungiyar dai ta shiga yajin aikin ne a ranar Larabar da ta gabata sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatunta.
Shugaban NARD ya ce: “Za a sake nazarin ci gaba da daukar matakai a ranar 2 ga Yuni 2023 yayin babban taron kungiyar inda za a yanke shawarar aiwatar da mataki na gaba.”
A ranar 29 ga watan Afrilu ne kungiyar ta bai wa gwamnati wa’adin makonni biyu a biya mata bukatunta ko kuma ta tsunduma yajin aiki.