Wasu ‘yan bindiga da suka addabi al’umma a karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna sun kashe manoma tara tare da yin garkuwa da wasu uku a Unguwar Danko da ke kusa da kauyen Dogon Dawa a karamar hukumar a ranar Asabar.
An tattaro cewa manoman na aikin gonakinsu ne kawai ‘yan bindigar suka fito kwatsam suka fara harbin duk wanda suka gani.
Zababben dan majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Kakangi Yahaya Musa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce duk wadanda aka kashe manoma ne, kuma wadanda suka samu raunukan harbin bindiga an garzaya da su asibiti domin yi musu magani.
“Eh, an tabbatar min da safiyar Lahadin nan cewa ‘yan bindiga sun kashe manoma tara a Unguwar Danko kusa da kauyen Dogon Dawa a ranar Asabar da tsakar rana, wasu kuma sun tsira da raunukan harbin bindiga,” inji shi.