An gudanar da taron kasa da kasa na karawa juna sani, albarkacin bikin cika shekaru 60 da fara tura likitocin kasar Sin zuwa nahiyar Afirka, inda a yayin taron na jiya Alhamis, wanda ya gudana a birnin Beijing, aka bayyana cewa, cikin shekaru 60 din da suka gabata, rukunonin likitocin Sin da aka tura kasashen waje domin ba da agajin kiwon lafiya, wadanda yawan su ya kai 30,000 sun yi aiki a kasashe da yankuna 76, kuma adadin marasa lafiya da likitocin suka yi wa jinya ya kai mutum miliyan 290.
Mashirya taron sun bayyana cewa, a yanzu haka, rukunonin irin wadannan likitoci na Sin na gudanar da ayyuka a cibiyoyi 115 dake kasashe 56, kuma kusan rabin su na aiki ne a yanayi mai tsanani a kuma wurare masu wuyar shiga.
Da yake tsokaci kan hakan, babban daraktan cibiyar binciken harkokin bunkasa kiwon lafiya ta kasar Sin Fu Qiang, ya ce kama daga yaki da cutar Ebola, da zazzabin shawara, zuwa kandagarki da shawo kan cutar COVID-19, da sauran cututtuka masu yaduwa, mambobin tawagogin jami’an lafiya da Sin ke aikewa kasashen waje, suna gudanar da hadin gwiwa da kasashen da ake gudanar da ayyukan, wajen inganta dabarun gano cututtuka da na magance su, matakin da ke samun yabo daga al’ummun dake cin gajiyar shirin.
A nasa bangare kuwa, daya daga manyan masu bincike a cibiyar nazarin kiwon lafiya da yawan jama’a ta Sin Gan Ge, cewa ya yi baya ga kokarin da wadannan tawagogi na likitocin kasar Sin suka yi a fannin fadada damar samun jinya ga al’ummun kasashen Afirka, da kara kyautata hidimomin kiwon lafiyar al’umma, a hannu guda kuma, sun yayata amfani da salon jinya da kiwon lafiya irin na kasar, matakin da ya bunkasa hulda da ma hadin gwiwa dake tsakanin Sin da kasashen Afirka. (Saminu Alhassan)