A ranar 4 ga wata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani game da shawo kan sinadarai masu alaka da sinadarin Fentanyl. Takardar ta yi cikakken bayani kan yadda kasar Sin ta gudanar da aikin shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, da nasarorin da ta cimma, yayin da gabatar da fasahohin kasar Sin wajen gudanar da ayyukan da abin ya shafa.
Dangane da wannan takardar da kasar Sin ta fidda, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana cewa, takardar za ta ba da taimako ga al’ummomi da gamayyar kasa da kasa wajen kara musu fahimtar matsayin kasar Sin kan wannan batu, da matakan da Sin ta dauka, da kuma nasarorin da Sin ta cimma a wannan fanni. Kasar Amurka ta yada jita-jita kan batun Fentanyl domin bata sunan kasar Sin, tare da kara haraji kan hajojin kasar Sin bisa wannan hujja. Babu sanin ya kamata cikin wannan lamarin. Amurka ta cutar da wasu da kai karan kanta.
- Xi Jinping Ya Halarci Bitar Tawagar Lardin Jiangsu
- Xi Jinping Ya Halarci Bitar Tawagar Lardin Jiangsu
A sa’i daya kuma, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen habaka hadin gwiwar dake tsakaninta da Amurka bisa ka’idar nuna adalci da girmama juna, kuma tana adawa da dukkan irin matakan da Amurka ta dauka domin matsa wa kasar Sin lamba, bisa hujjar batun Fentanyl. Sin ta bukaci Amurka da ta mutunta gaskiya, da kare moriyar kanta yadda ya kamata, domin gudanar da harkoki ta hanyoyi masu dacewa.
Lin Jian ya kara da cewa, Amurka ta sake kara haraji kan hajojin Sin bisa hujjar batun Fentanyl, kana, sau da dama, kasar Sin ta nuna adawa kan wannan batu. Dukkanin matakan mayar da martani da kasar Sin ta dauka sun kasance matakan da suka wajaba kuma masu dacewa domin kare moriyar kasa. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp