• English
  • Business News
Monday, October 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Liu Guizhen: Rayuwa Za Ta Yi Dadi Da Ma’ana Idan Aka Yi Kokarin Taimakawa Masu Bukata

by CMG Hausa
3 years ago
Liu Guizhen

Liu Guizhen, wata mambar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ce a gundumar Daixian ta birnin Xinzhou dake lardin Shanxi na arewacin kasar Sin. Ta rike mukaman da suka hada da shugabar reshen jam’iyya a kauye, daraktar kwamitin kauye, kuma malama, haka kuma likita a cikin shekaru 40 da suka gabata. Liu ta taba tambayar mahaifinta abun da ya kamata ta yi don zama cikakkiyar ’yar jam’iyya. Inda ya ba ta amsa da cewa, “ki rika tunanin sauran jama’a a zuciyarki, kuma ki yi iya kokarinki wajen taimaka musu”. Kuma wannan ya kasance burin da uban da ’yarsa suka sanya gaba.

Taron da ake a garin dake makwabtaka da su zai kare da tsakar rana. Kuma ana kammalawa, Liu Guizhen ta gaggauta komawa kauyensu don tattauna batun kyautata muhalli da sauran mambobi. Bayan nan, ta taimaka wajen auna yanayin hawan jinin sauran mutanen kauyen. Daga irin wadannan ayyuka, mutum zai iya gane yanayin rayuwar Liu mai cike da hada-hada.

Liu Guizhen
•Liu Guizhen tana tattaunawa da jami’in kauye game da aikin gona

An haifi Liu Guizhen a Duanjiawan, wani karamin kauyen dake kusa da tsaunin Nanshan dake gundumar Daixian. Mahaifinta Liu Baixiao, ya shiga JKS ne a shekarar 1943, kuma ya zama sakataren reshen jam’iyyar na farko dake kauyen a shekarar 1946.

“Ke kadai ce kika yi babbar sakandare. Wa kike tsammanin zai yi ayyukan?” Abun da Liu Baixiao ya taba tambayar ’yarsa ke nan.
Kalaman mahaifinta sun zaburar da ita wajen daukar nauye-nauye. Liu Guizhen ta hakura da damar da ta samu na shiga jami’a, kuma a 1978 ta zama likitar kauye, domin ta kula da al’umma.
Shekaru 10 bayan nan, aka sauyawa malami daya tilo na kauyen wajen aiki.
“Kawai ki rika koyarwa kafin sabon malami ya zo. Ba za a jima ba”, cewar mahaifinta. Bisa kwarin gwiwar da ta samu daga mahaifinta, Liu ta kara daukar nauyin zama malama.
A 1996, aka zabi Liu Guizhen a matsayin sakatariyar reshen jam’iyya na kauyen. A shekarar 2003 kuma aka zabe ta matsayin daraktar kwamitin kauye.

A baya, mazauna kauyen kan je asibiti ne idan ba su da wata mafita, saboda ba za su iya biyan kudin asibitin ba. Samun Likita a kauyen, dadadden burin bai daya ne na al’ummar.
Bisa la’akari da wannan yanayi, Liu Guizhen ta tafi birni, ta karanci fannin likitanci. Rabin shekara bayan nan, ta kammala karatunta ta koma kauyen, inda ta fara duba marasa lafiya.

LABARAI MASU NASABA

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

Liu Guizhen
•Liu Guizhen tana tattaunawa da wata mara lafiya a kauye

A shekarun da suka biyo baya kuma, ta mayar da hankali wajen gudanar da bincike, inda kwarewarta na aikin likitanci ya inganta. Ta koyawa kanta yadda ake acupuncture kuma tana yawan amfani da wannan dabara ta likitancin gargajiya na kasar Sin domin kula da marasa lafiya a kyauta. Wani lokacin ma da kudinta take sayawa mutane masu bukata magani.

A wani lokaci, wani mara lafiya mai suna Chen Zhiliang, ya kashe kudin da ya kai sama da yuan 30,000 kwatankwacin dala 4,607 a asibiti, lamarin da ya haifar da matsin rayuwa ga iyalinsa. Sai Liu Guizhen ta taimakawa Chen, inda aka mayar masa da kudinsa karkashin shirin inshorar lafiya na gamayya na kauyen.
Tsarin inshorar lafiya na kauye da gwamnatin kasar Sin ta aiwatar a 2003, na da nufin tabbatar da cewa mazauna kauyuka na samun hidimomin kiwon lafiya ba tare da sun kashe kudadensu ba. Da farko, galibin mutanen kauyen sun ki biyan kudin da ake bukata na shiga inshorar. Don haka, Liu ta yi amfani da kudinta wajen biyawa wasu daga cikinsu. Amma bayan an mayarwa Chen kudin da ya kashe a asibiti, sai karin mutane suka shiga shirin.
Mazauna kauyukan dake kewaye da su, sun bukaci ta rika duba iyalansu. Tazarar dake tsakanin gidan Liu Guizhen da kauye mafi nisa ya kai sama da kilomita 5. A baya, babu tituna masu kyau da kekuna za su bi cikin sauki, don haka, sai ta bi hanyoyin dake cike da tsaunika. Wani lokaci, ta kan kwana a gidajen marasa lafiya saboda ta yi dare.

“Na koyi dabarun da suke da amfani ga mutane, don haka ina son zama mai hidimta musu”, cewar Liu Guizhen.
A shekarar 1998, malami daya tilo na kauyen ya tafi. Saboda nisan kauyen da rashin kyan muhalli, wasu malamai ba sa son zuwa. Sai iyaye suka fara damuwa da dakatarwar da aka yi na karatu. A nan ma, sai Liu Guizhen ta cike gurbin da aka samu.

Ta mayar da gidanta zuwa aji a lokacin da ake sake fasalin makarantar, kuma ta yi amfani da duk wani abu da za ta iya, ciki har da teburi da gado da allo, domin koyarwa da daliban.

Liu Guizhen
Liu Guizhen na tattaunawa da mara lafiya.

An kammala ginin makarantar a kan lokaci domin fara sabon zangon karatu. Sai dai, kauyen bai samu damar daukar sabon malami ba. Liu Guizhen ta ci gaba da cike wannan gurbi. Ta koyar da harshen Sinanci da lissafi da kimiyya da sauran wasu darussa ga daliban dake aji 1 zuwa 5.

A shekarar 2006, aka samu sabon malamin da zai yi aiki a makarantar firamare. Sai dai kuma an samu karin dalibai, lamarin da ya kai ga bukatar malamai biyu. Don haka, Liu Guizhen ta sake daukar wannan nauyi.
Ta kan sayi kayayyaki kamar toilet paper da fensira, ga yaran da suke bukata. Saboda kokarinta, babu wani dabili da ya daina zuwa makaranta. Dayawa daga cikin dalibanta sun kammala makarantar midil, yayin da wasu kuma suka shiga Jami’a.

“Na gaza shiga jami’a,” cewar Liu Guizhen. “yaran sun taimaka min cimma burina.”
Ban da wannan kuma, Liu Guizhen ta kan yi tafiye-tafiye akai-akai zuwa wasu yankuna domin nazartar yanayin da suke ciki, ta yadda za ta iya taimaka musu samun karin kudin shiga.
Bisa la’akari da yanayin shimfidar yankin, da sauran wasu batutuwa, Liu Guizhen ta yanke shawarar tattara jama’a domin noman itacen Pinus Tabulaeformis a bakin kogi.
“Da farko, mutanen kauyen na tsoron yin asara, don haka babu wanda ya gwada”, cewar Liu Guizhen, “kawai ina son samar musu mafita ne”.

Liu Guizhen da maigidanta, Yang Hongsheng, sun jagoranci shuka a wuri mafi dacewa a bakin kogi. Bayan shekaru 2 suna kula da shukar, iccen ya girma da kyau. Cikin lokacin bazara na 3 bayan shukar, Liu Guizhen ta sayar da wasu daga cikin itatuwan, kuma ribar da ta samu ya zarce wanda ake samu daga noman alkama da masara.

Nan da nan labarin nasarar Liu Giuzhen ya karade kauyen. Ta bi gida-gida domin tattaunawa da mutanen kauyen game da sana’ar, da kuma taimakawa masu da shawarar zabar wuri mafi dacewa da sayen irrai da taki.
Karkashin jagorancin Liu Guizhen, galibin mutanen kauyen suka fara shuka irin. A shekarar 2017, ta kafa wata kungiyar gama kai don inganta sana’ar, kuma ta fadada ta zuwa kauyuka makwabta.
Liu Guizhen ta yi iyakar kokarin kirkiro damarmakin kasuwanci ga ‘yan uwanta mutanen kauyen. Itatuwan magungunan gargajiya na tsirowa a kan duwatsu a fadin kauyen. Don haka ta karfafawa mutanen kauyen gwiwar hawa tsaunika don tsinko irin wadannan magunguna domin su sayar.
Kudin shigar mutanen kauyen ya yi ta karuwa ta hanyar gwada abubuwa. Galibinsu sun sayi sabbin gidaje a gundumar, kuma sun fara rayuwa irin ta birni.
“Rayuwa za ta yi dadi da ma’ana idan ka yi kokarin taimakawa sauran mutane”, cewar Liu Guizhen, “Wannan ba gadon dabi’un iyalina ba ne kadai, wata ka’ida ce da na kafawa kai na. A kullum mahaifina na koya min tunawa da mutane a zuciyata, kuma na koyar da ‘ya’yana hakan ni ma.”
Yang Junyu, babbar diyar Liu Guizhen, ta taba aiki a matsayin nas a wani asibitin dake lardin Shandong na gabashin kasar Sin. Ta sha yi wa mahaifiyarta magiyar daukar hutu ta kai mata ziyara gidanta. Sai dai Liu Guizhen ba ta da lokacin hutu. Kuma ba za ta taba barin kauyen ba muddin ana bukatarta.

“Idan na tsaya a kan mumbari, to ni malama ce. A wajen aji kuma, ni likita ce. A matsayin daraktar kwamitin kauyen kuma shugabar reshen jam’iyyarmu a kauyen, zan rika tunawa da aminta da ni da jama’a suka yi da kuma nauyin dake wuyana”, kamar yadda Liu Guizhen ta fada.
Liu Guizhen ta karbi lambobin yabo da dama saboda irin kokarinta da jajircewa.
(Faeza Mustapha daga Beijing, China)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya
Daga Kasar Sin

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

February 28, 2025
Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin
Daga Kasar Sin

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

July 14, 2024
wang lili
Daga Kasar Sin

Yadda Wang Lili Ke Kiyaye Neman Cimma Nasara A Wasan Kwallon Kwando

July 6, 2024
Next Post
APC

Wainar Da Aka Toya A Zaben Dan Takarar APC Na Shugaban Kasa

LABARAI MASU NASABA

Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina

Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina

October 12, 2025
Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

October 12, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi ASUU Kan Yajin Aiki, Ta Ce “Babu Aiki, Babu Albashi”

Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi ASUU Kan Yajin Aiki, Ta Ce “Babu Aiki, Babu Albashi”

October 12, 2025
An Wallafa Ra’ayoyin Shugaba Xi Kan Batutuwan Da Suka Shafi Mata Da Yara Cikin Karin Harsunan Waje

An Wallafa Ra’ayoyin Shugaba Xi Kan Batutuwan Da Suka Shafi Mata Da Yara Cikin Karin Harsunan Waje

October 12, 2025
Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba

Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba

October 12, 2025
Jami’ar MDD: Taron Kolin Matan Duniya Ya Zo Daidai Lokacin Da Ya Dace

Jami’ar MDD: Taron Kolin Matan Duniya Ya Zo Daidai Lokacin Da Ya Dace

October 12, 2025
An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro

An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro

October 12, 2025
Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan

Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan

October 12, 2025
Yaushe Lamine Yamal Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?

Yaushe Lamine Yamal Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?

October 12, 2025
Sharhi: Lai Qingde Ba Zai Iya Jirkita Gaskiya Ba

Sharhi: Lai Qingde Ba Zai Iya Jirkita Gaskiya Ba

October 12, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.