Da yammacin yau Litinin ne aka gudanar da taron manema labarai na taro na uku, na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ko CPPCC karo na 14, inda mai magana da yawun taron Liu Jieyi, ya gabatar da yanayin taron ga kafofin watsa labarai na kasar Sin da na waje, tare da amsa tambayoyin manema labarai.
A fannin gudanar da ayyuka da ba da shawarwari, Liu Jieyi ya gabatar da cewa, CPPCC ta mai da hankali kan batutuwa masu muhimmanci da wahala, da suka hada da inganta zamanantarwa irin ta Sin, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali na zamantakewar al’umma, kuma ta gudanar da ayyuka da suka shafi tattauna batutuwan siyasa guda 85, da aiwatar da shawarwari sama da 5000, da kuma gabatar da bayanai sama da dubu 10.
- CMG Zai Watsa Bikin Bude Zama Na Uku Na Majalisar CPPCC Karo Na 14
- Kano Pillars Ta Koma Ta 4 A Teburin Firimiyar Nijeriya
Ya ce kowane kwamiti na musamman na majalisar ya yi amfani da karfinsa don tsara aikin shigar mambobi sassan kauyuka, da masana’antu, da makarantu, da unguwannin birane, don tattara ra’ayoyi da shawarwari daga kowane bangare, wadanda suka ba da hidimomi ga jam’iyya da gwamnati, wajen aiwatar da manufofin siyasa, wanda hakan ya nuna muhimmiyar rawar da CPPCC ke takawa a cikin tsarin mulkin kasa.
Yayin da aka ambato halin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki, Liu Jieyi ya ce, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba mai inganci a shekarar 2024, inda GDPn kasar ya zarce yuan triliyan 134, kuma saurin karuwarsa ya kai 5%, wanda ya kasance a sahun gaba cikin manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp