Zakarun gasar Firimiya ta kasar Ingila, Liberpool za su karbi bakuncin Bournemouth a makon farko na bude gasar Firimiya ta 2025-26, inda Manchester United za ta kara da Arsenal a Old Trafford, Liberpool, wacce ta lashe gasar a kakar wasa ta farko ta sabon kocinta Arne Slot, za ta fara kare kambunta a Anfield a ranar Juma’a, 15 ga watan Agusta.
Sunderland wacce ta dawo buga gasar a karon farko tun daga 2016-17, za ta fara kamfen din ta a gida da West Ham, ranar Asabar 16 ga watan Agusta 2025, sai Leeds United wadda ta lashe gasar Championship ta yi maraba da Eberton a Elland Road a daren Litinin, yayin da Burnley za ta tafi gidan Tottenham mai rike da kofin Europa, wanda kuma zai zama wasa na farko da sabon kocin Tottenham Thomas Frank zai jagoranci kungiyar ta birnin Landan.
- Hukumar NPA Ta Bayar Da Kwangilar Aikin Ruwa Na Tashar Lekki
- Wani Injin Jirgi Mai Saukar Ungulu Kirar Kasar Sin Ya Samu Shaidar Amincewa
Magoya bayan Eberton za su jira har zuwa wasan mako domin buga wasan farko a sabon filin wasanta na Hill Dickinson, inda za su kara da Brighton, Manchester City ta Pep Guardiola za ta yi fatan dawowa gasar Firimiya bayan rashin lashe kowane irin kofi a kakar wasan da ta gabata da fara wasa da Wolberhampton Wanderers a filin wasa na Molineud.
Sabuwar kakar wasan, wadda ta kunshi wasanni 380, za a kammala ranar Lahadi, 24 ga Mayu, 2026, Hukumar gasar Firimiya ta ce za a fara wannan kakar ranar 15 ga Agusta, kwanaki 82 kenan da kammala karshen kakar wasa ta shekarar 2024-25.
Ga Jerin Wasannin Makon Farko Na Gasar Firimiya Ta Badi
Juma’a, 15 ga Agusta
Liberpool bs Bournemouth
Asabar, 16 ga Agusta
Aston Billa bs Newcastle
Brighton Bs Fulham
Nottingham Forest bs Brentford
Sunderland bs West Ham
Tottenham Bs Burnley
Wolberhampton Wanderers bs Manchester City
Lahadi, 17 ga Agusta
Chelsea bs Crystal Palace
Manchester United bs Arsenal
Litinin, 18 ga Agusta
Leeds Bs Eberton
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp