Babban sufeton ‘yan Sandan Nijeriya Ibrahim Idris, ya ce lokaci bai yi ba da za’a kafa rundunar ‘Yan Sandan Jihohi domin samar da tsaro, saboda irin matsalolin siyasar da ake fuskanta a kasar.
Ibrahim Idris ya bayyana hakanne yayin da ya ke gabatar da kasida ga taron gwamnonin jihohin kasar da suka kafa kwamitin don nazarin bukatar haka.
Sufeton, sakamakon irin yanayin siyasar da kasar ke ciki da kuma fargabar yadda masu mulki za su iya yin amfani da ‘yan Sandan wajen musguna wa abokan hamayya, ‘a cewarsa lokacin bayar da damar fara amfani da wannan tsari a jihohi bai yi ba’inji shi.
Shugaban ‘yan sanda ya bukaci gwamnati da ta inganta rundunar da ake da ita a yanzu wajen taimaka ma ta da kayan aiki da kuma isassun kudade domin aiwatar da aikin da ke gabanta.