Jagoran jam’iyyar APC na kasa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis, ya gargadi wakilan jam’iyyar daga jihar Ogun da su mara masa baya a babban taron jam’iyyar na kasa mai zuwa zuwa na zaben shugaban kasa na shekarar 2023.
Tinubu, wanda ya yi jawabi ga wakilan jam’iyyar a Abeokuta, babban birnin jihar, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da ya kamata ya ci ribar ayyukansa da sadaukarwa wajen gina babbar jam’iyyar siyasa.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya fito ne daga jihar Ogun.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya tunatar da cewa ya marawa ‘yan siyasar Nijeriya da dama baya don ganin sun cimma burinsu na siyasa, inda ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na daya daga cikin irin mutanen da ya goyawa baya.
Ya kuma bayyana cewa irin su Nuhu Ribadu da Atiku Abubakar a lokacin da tsofaffin jam’iyyunsu na siyasa suke ya yi musu hidima, ya kuma bayyana cewa a baya ya samar da tsarin siyasa da dama don tsayawa takarar shugaban kasa.
Tinubu ya bayyana cewa bai taba yin nadamar sadaukarwar da ya yi wa Osinbajo ba, ta damar da ya ba shi ta zama mataimakin shugaban kasa ga shugaba Buhari ba, a yayin da ake shirin tunkarar zaben shugaban kasa na 2015.
“A yanzu sama da shekaru 25 ina bautar wadannan ’yan siyasa maza da mata, har ma da Shugaban kasa,”
“Ban da irin gudunmawarmu da Buhari bai samu nasarar lashe wancan zaben na shugaban kasa a 2015 ba bayan yunkurin da ya yi sau uku ba tare da goyon bayana ba”.
“Tun da Shugaba Buhari ya hau mulki ban karbi mukamin minista ko jakadanci ba, amma yanzu lokaci na ne, goyon bayana ga wadannan ‘yan siyasa maza da mata ya isa, ba na son shiga cikin tarihin siyasa mai ban tausayi a cikin Najeriya, na zo ne domin neman kuri’un ku.”