• English
  • Business News
Tuesday, November 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Lokaci Ya Yi Da Za A Samar Da Rumbun Bayanai Na Bai-ɗaya A Nijeriya – CGI Isah Jere

by Abdulrazaq Yahuza
3 years ago
Bayanai

Shugaban Hukumar Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS) Isah Jere Idris ya yi kiran samar da haɗin kai a tsakanin hukumomin tattara bayanai a ƙasar nan don cimma nasarar samar da rumbun bayanai na bai-ɗaya na Nijeriya domin haɓaka ci gaban ƙasa.

Ya yi wannan kiran ne a hedikwatar hukumar ta shige da fice yayin da yake karɓar baƙoncin tawagar gudanarwa na Shirin Bunƙasa Samar Da Bayanan Shaida Domin Ci Gaba (DID4D) a ziyarar ban girma da suka kai masa.

  • Ba Zan Raga Wa ‘Yan Bindiga Ba Sai Na Ga Bayansu – Buhari 

Sanarwar da ta fito daga Jami’in Sadarwa na NIS, ACI Amos Okpu, ta yi bayanin cewa shugaban hukumar, CGI Isah Jere ya jaddada muhimmiyar rawar da tattara bayanai da sarrafa su za su taka a kan sha’anin tsaro da tsare-tsaren ƙasa.

“Muna rayuwa ne a lokacin da bayanai suka zama wata babbar kadara don ƙarfafa ƙasa kuma haƙiƙa sashen bayanan yana gwagwarmayar ƙwace wa arzikin mai kambunsa na kawo arziki a duniya; don haka akwai bukatar mu haɗa kai don inganta bayanan ƙasa. Ba za mu iya ci gaba da yin watsi da bayananmu suna zaune kara-zube a cikin rumbunan adana su ba a tsakanin hukumomi daban-daban. Lokacin daidaita su su zamo bai-ɗaya ya yi”, in ji shi.

Kwanturola Janar ɗin ya ci gaba da cewa, hukumar a matsayinta na mai taka muhimmiyar rawa a tsarin bayanan ƙasa tun daga shekarar 2019 ta nuna ƙwarin gwiwa wajen cimma daidaiton tsarin bayanan ‘yan ƙasa tare da ɓullo da ingantaccen fasfo na zamani (ePassport) wanda ya wajabta bayar da lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) ga duk mai neman fasfon.

LABARAI MASU NASABA

Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano

Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo

Ya kuma lura cewa hukumar ta NIS tana ci gaba da zuba jari a tsarin tattara bayanai da sarrafa bayanan ta na’urorin da take aiki da su a sassa daban-daban da suka haɗa da Kan Iyakoki don tabbatar da ingantaccen tsarin bayanai. Ya ba da tabbacin cewa NIS za ta ci gaba da kasancewa a shirye a koyaushe don yin haɗin gwiwa tare da hukumomin da abin ya shafa don cimma cikakkiyar daidaituwar bayanan shaida na ƙasa don gudanar da kyawawan tsare-tsare da ci gaban ƙasa.

Bayanai
CGI Isah Idris Jere (a tsakiya) Shugaban Shirin DID4D, Mista Solomon Musa (na biyar daga dama) da sauran mahukuntan shirin da na NIS a yayin ziyarar na haɓaka samar da bayanai

Tun da farko, Babban Jami’in Gudanarwa na DID4D, Mista Solomon Musa Odole ya sanar da cewa tawagarsa ta ziyarci hedkwatar NIS ce don neman haɗin gwiwa kan aikin tantance bayanan shaida a zamanance.

Ya bayyana ƙudirin tawagarsa ta tattaunawa mai ma’ana tare da haɗin gwiwa da NIS don cimma burin Gwamnatin Tarayya na haɓakawa da ƙarfafa tsarin da ake amfani da shi na tattara bayanan shaida da nufin ƙara yawan mutanen da ke da takardar shaidar ƙasa.

A cewarsa, yin hakan zai ƙara sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa damar samun muhimman ayyuka, da inganta hanyoyin samar da ayyuka da kuma ƙarfafa tattalin arzikin Nijeriya ta fuskar zamani.

Ya ci gaba da cewa, ana ci gaba da ƙoƙari sosai ciki har da tattaunawa kan manufofin ƙasa da masu ruwa da tsaki wajen samar da dokar kare bayanan sirri ta ƙasa ko sake duba dokokin da ake da su domin tabbatar da cewa an samar da tsare-tsare na hukumomi da suka dace don ciyar da tattalin arzikin ƙasa gaba.

Shirin DID4D dai wani shiri ne na Nijeriya, wanda Bankin Duniya, da Bankin Zuba Jari na Turai da Hukumar Raya Faransa suka ɗauki nauyin gudanar da shi da nufin ƙara yawan mutanen da ke da Lambar Shaida ta ƙasa (NIN) da aka samar ta sahihiyar hanya mai ƙarfi.

  • https://ha.m.wikipedia.org/wiki/Bayanai

Babban jami’in shirin ya samu rakiyar sauran ma’aikatan shirin da suka haɗa da Dakta Walter Duru, Manajan Sadarwa na cikin gida, Bamidele Akinola, Akantan Shirin da Mouktar Adamu, Manajan Sadarwa da dai sauransu.

NIS dai ta duƙufa ka’in da na’in wajen tabbatar da bayanan duk wasu harkoki na shige da fice da suka shafi baƙi da ‘yan ƙasa. Inda ta samar da na’urorin tattara bayanan da tantance su a filayen jiragen sama da iyakokin ruwa da na kan-tudu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano

November 10, 2025
Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo
Manyan Labarai

Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo

November 10, 2025
Gwamnati Ta Nemi Ƴan Nijeriya Su Ƙwantar Da Hankali Kan Barazanar Trump
Manyan Labarai

Gwamnati Ta Nemi Ƴan Nijeriya Su Ƙwantar Da Hankali Kan Barazanar Trump

November 10, 2025
Next Post
Kotun Birtaniya Ta Bada Belin Matar Ekeweremadu

Kotun Birtaniya Ta Bada Belin Matar Ekeweremadu

LABARAI MASU NASABA

An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin 

An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin 

November 10, 2025
Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin

Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin

November 10, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano

Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano

November 10, 2025
Sin Ta Dakatar Da Jiragen Ruwan Amurka Daga Biyan Kudi Na Musammam A Tashoshinta Na Ruwa

Sin Ta Dakatar Da Jiragen Ruwan Amurka Daga Biyan Kudi Na Musammam A Tashoshinta Na Ruwa

November 10, 2025
Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa

Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa

November 10, 2025
Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo

Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo

November 10, 2025
Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin

Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin

November 10, 2025
Gwamnati Ta Nemi Ƴan Nijeriya Su Ƙwantar Da Hankali Kan Barazanar Trump

Gwamnati Ta Nemi Ƴan Nijeriya Su Ƙwantar Da Hankali Kan Barazanar Trump

November 10, 2025
Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo

Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo

November 10, 2025
FCT Ta Saka Ranar 1 Disamba Don Kammala Biyan Kudin Hajjin 2026 N7.7m

FCT Ta Saka Ranar 1 Disamba Don Kammala Biyan Kudin Hajjin 2026 N7.7m

November 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.